Atiku Abubakar yayi nasara a karamar hukumar Kaura a Kaduna

Atiku Abubakar yayi nasara a karamar hukumar Kaura a Kaduna

Mun samu labari cewa ‘dan takarar babbar jam’iyyar adawa na PDP watau Alhaji Atiku Abubakar ya samu nasara a karamar hukumar farko da sakamakon zaben ta ya fito fili daga cikin jihar Kaduna.

Atiku Abubakar yayi nasara a karamar hukumar Kaura a Kaduna
Sakamakon zaben Kaduna ya fara fitowa bayan dogon lokaci
Asali: Twitter

Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 33, 647 a cikin karamar hukumar Kaura da ke yankin kudancin Kaduna. Malamin zabe na yankin watau Farfesa Nafiu Abdu ya bayyana wannan sakamako dazu nan.

Kamar yadda hukumar zaben ta tabbatar, shugaba Muhammadu Buhari ya samu kuri’u 6, 907 ne rak a garin na Kaura. Kusan dai mutane 44, 000 ne su ka kada kuri’ar su a karamar hukumar a zaben da aka gudanar tun jiya.

KU KARANTA: Sakamakon zaben shugaban kasa da kuma Majalisa daga Jihar Kaduna

Jami’in INEC Luka Maude, ya sanar da zaben majalisa inda yace PDP ta samu kuri’a 21. 187 yayin da Sunday Aso ya tashi da kuri’u 6, 854. Sauran ‘yan takarar sun hada da Afang Tanda, Zamnai Joseph da Simon Na’Allah.

Haka zalika Sanata Danjuma La’ah na PDP ya samu kuri’a 29, 356 a cikin Garin Kaura. Shi kuma Bala Bentex ya samu kuri’u 9, 071. Jam’iyyar adawa ta SDP da kuma PRP sun samu kuri’u 1, 102 da 1, 389 ne a cikin karamar hukumar.

Yanzu kuma mu ke jin cewa shugaba Muhammadu Buhari ne yayi nasara a cikin karamar hukumar Giwa inda ya tashi da kuri’u 45, 574. Atiku Abubakar na PDP ya samu kuri’u 9, 838 ne a wannan yanki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel