'Kaddara ta riga fata: Miji na ya zama shugaban kasa - Titi Abubakar
- Uwargidan dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ta ce Ubangiji ya kaddara Atiku ya zamto shugaban kasa
- Titi Abubakar ta ce nasarar Atiku a yayin zaben fidda gwanin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP wata manuniya ce da ke haskaka makomar da Uabangiji ya yi masa tanadi
- Matar Wazirin Adamawa ta jaddada yakinin ta dangane da yadda Atiku zai fidda kasar nan zuwa tudun tsira yayin da kasance jagoran kasar nan
Titi Abubakar, daya daga cikin Matan dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ta ce ba bu wata makawa Mijin ta zai zamto shugaban kasar Najeriya a yayin babban zabe da za a gudanar a ranar Asabar ta mako mai zuwa.
Mai dakin tsohon mataimakin shugaban kasar ta bayyana cewa, ƙaddara ta rigayi fata akan Mijin ta ya zamto shugaban kasar Najeriya domin jagorantar kasar nan yayin babban zaben kujerar shugaban kasa da za a gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu.
Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Titi ya yi ziyarar ban girma da ta kai fadar wani babban jigo kuma madugu na jam'iyyar PDP, Cif Bode Olajumoke a jihar Legas, ta misalta Atiku a matsayi kaddarawar Ubangiji da zai zamto shugaban kasar nan.
Ta ce nasarar Mai gidan ta a yayin zaben fidda gwanin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da aka gudanar cikin birnin Fatakwal na jihar Ribas a wata Oktoba na shekarar da ta gabata, wata manuniya ce da ke haskaka ƙaddarawar Ubangiji na samun nasarar sa a zaben bana.
KARANTA KUMA: CIkin Hotuna: Ganawar Atiku da manyan kungiyoyi 3 a jihar Benuwe
Matar Wazirin Adamawa ta ce, Ubangiji ya ƙaddara mijinta ya zamto wanda zai fidda kasar nan zuwa tudun tsira ta hanyar ceto ta daga kangin da ta afka a halin yanzu. Ta kuma jaddada yakinin ta dangane da yadda Mata da Matasa za su ci moriya a karkashin gwamnatin sa.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng