Arewa
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ce matakan da gwamnatinsa ta ɗauka tun da ya karɓi mulki sun taka rawa wajen inganta tsaro fiye da yadɗa ya tarar a jihar.
Mai martaba sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya gayyaci manyan malamai an yi taron addu'a ga shugaban ƙasa Tinubu, gwamnan Kwara da Najeriya.
Gwamna Dauda Lawal ya ce ya tarar da asusun gwamnatin Zamfara ba kudi, sai wata N4m. Amma ya ce yanzu ya biya basussukan albashi, NECO, WAEC da na wuta.
Bayan Sarkin Hausawa a Enugu ya karbi muƙami a gwamnati, matasan Arewa a jihar sun soki basaraken, Yusuf Sambo II, bisa amincewa da mukamin hadimin gwamna.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kafa tarihi a fannin hakar ma'adanai a Najeriya. Gwamnan ya kafa masana'antar sarrafa lithium ta farko a kasar nan.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa wasu fusatattun matasa a garin Tsiga da ke jihar Katsina sun kone fadar dagacin garin bayan wani barawo ya nemi mafaka.
Ƙungiyar ta bukaci Tinubu ya kori Badaru daga ministan tsaro saboda kara tabarbarewar tsaro a kasar nan. Ta soki naɗinsa, tana mai cewa kwata kwata bai cancanta ba.
Za ku ji cewa Hakeem Baba-Ahmed ya ce ‘yan siyasa na yanzu na nemawa kansu mafita ne kawai,kuma talaka ya gaji, saboda haka zai nemi ‘yancinsa a zaben 2027.
An gabatar da kudirin karba-karba na shugaban kasa da mataimakinsa a yankuna shida na inda majalisar ta ƙi amincewa da kudurin dokar sauya kundin tsarin mulki.
Arewa
Samu kari