Abin da Malaman Musulunci Suka Yi wa Tinubu da Mai Martaba Sarki Ya Tara Su a Fada

Abin da Malaman Musulunci Suka Yi wa Tinubu da Mai Martaba Sarki Ya Tara Su a Fada

  • Mai martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya shirya taron addu'a domin neman taimakon Allah a halin da ake ciki a ƙasar nan
  • Sarkin ya haɗa manyan maluman addinin musulunci a fadarsa kuma an yi addu'o'in neman zaman lafiya da samun nasarar shugabanni
  • Wakilan gwamnatin Kwara sun halarci wurin addu'ar da aka yi wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu da Gwamna AbdulRahman AbdulRazak

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ilorin, Kwara - Fitattun malaman addinin Musulunci daga sassa daban-daban na jihar Kwara sun halarci taran addu'a a fadar mai martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari.

Sarkin Ilorin ya gayyaci malaman ne domin gudanar da taron addu’ar neman zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

Sarkin Ilorin.
Sarkin Ilorin ya tara manyan malaman Musulunci, sun yi wa Bola Tinubu addu'a Hoto: Inside Ilorin
Asali: Twitter

Tinubu da gwamnan Kwara sun sha addu'a

Leadership ta rahoto cewa an shirya addu'ar ne domin neman Allah ya taimaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinsa na bude taron, Sarkin Ilorin wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Jihar Kwara, ya ce an shirya addu’ar domin rokon Allah ya dawo da zaman lafiya a sassan Najeriya.

Basaraken ya ƙara da cewa taron addu'o'in zai maida hankali kan neman Allah ya kawo karshen duk wasu rikice-rikice, tare da yi wa shugaban kasa da gwamnan Kwara fatan alheri.

Manyan malaman da suka je fadar Sarkin Ilorin

Babban Limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Soliu, ne ya jagoranci addu’ar, tare da manyan malamai irin su Imam Imale Sheikh AbdulHamid Abdullahi.

Sauran manyan maluman jihar Kwara da suka halarci wurin sun haɗa da Imam Gambari, Ajanasi da Alfa Rabana, Imam Yakubu Aliagan, babban Mufti na Ilorin, Sheikh Sulaiman Faruq Onikijipa da sauransu.

Gwamnan Kwara ya tura wakilai fadar Sarki

An samu wakilcin gwamnatin jihar Kwara a wajen addu’ar karkashin jagorancin mai ba gwamna shawara ta musamman, Alhaji Saadu Salahu.

Cikin tawagar akwai shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar, AbdulKadir Magaji, da hadiminn gwamna kan ayyuka na musamman, Alhaji AbdulRazaq Jiddah.

Sauran sune kwamishinan ilimi, Dr Olohungbebe, tsohon daraktan NNPCL, Dr Ghali Alaaya, da wasu manyan jami'an gwamnati, kamar yadda The Nation ta kawo.

Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, Alhaji Saadu Salahu ya bayyana cewa an gudanar da addu’o'in ne domin nasarar gwamnati mai ci a matakin tarayya da na jihar Kwara.

Sarkin Ilorin da Gwamnan Kwara.
Sarkin Ilorin ya jagoranci taron yi wa shugaban kasa da gwamnan Kwara addu'a Hoto: @RealAARahman
Asali: Facebook

Me yasa Mai martaba ya shirya taron addu'a?

Ya ce:

“Ilorin cibiyar ilimi ce a Musulunci, kuma Alkur’ani shi ne hasken da ya jagoranci kakanninmu. Fadar sarki wuri ne mai albarka wajen gudanar da addu’o’i.
"Mai martaba Sarki, wanda shi ne uba ga Gwamna AbdulRazaq, ya ga dacewar gudanar da wannan addu’a don nuna goyon baya ga kokarin shugaban kasa da gwamna wajen ci gaban Najeriya.”

Sarkin Ilorin ya yi wa ƴan siyasa nasiha

A wani labarin, kun ji cewa Mai martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bukaci ‘yan siyasar Najeriya da su kasance masu gaskiya da rikon amana.

Basaraken ya shawarci ƴan siyasa musamman shugabanni ko masu neman mulki da su daina yi wa jama'a ƙarya, su riƙa fadin gaskiya a koda yaushe.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar shugabannin jam’iyyar SDP ƙarƙashin jagorancin Prince Adewole Adebayo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262