An Sake Taso Tinubu a Gaba da Ya Yi Gaggawar Fatattakar Ministarsa daga Arewa
- Wani dan gwagwarmayar siyasa, Theo Agada, ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya sauke daya daga ministocinsa daga Arewa
- Agada ya bayyana cewa ministar al’adu da kirkire-kirkire, Hannatu Musa Musawa ba ta taka rawar komai ba tun da aka nada ta
- Duk da suka da ake yi mata, Musawa ta ce ma’aikatarta ta jawo jarin dala miliyan 300 kuma za a samar da ayyuka miliyan 2 a Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Wani dan gwagwarmayar siyasa, Theo Abu Agada, ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami ministarsa.
Agada ya roki Tinubu ya sauke Hannatu Musawa wacce ita ce ministar al’adu da kirkire-kirkire saboda rashin katabus.

Asali: Facebook
Hakan na cikin wani rubutu da Agada ya yi a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka taso wasu ministocin Tinubu a gaba
Yawan kiraye-kirayen cire wasu ministoci da ake cewa ba su da tasiri sai karuwa yake yi daga sassa daban-daban na kasa.
Ministoci da dama suna fuskantar irin wannan matsin lamba daga yan kasa ko wasu kungiyoyi saboda zargin rashin tsinana komai.
Daga cikin ministocin akwai na tsaro, Mohammed Badaru Abubakar da mataimakinsa a ma'aikatar, Dr. Bello Matawalle.

Asali: Twitter
An buƙaci Tinubu ya kori Hannatu Musawa
Duk da cece-kuce da ke kewaye da ita, Musawa ta tsallake sauye-sauyen ministoci da Shugaba Tinubu ya yi a watan Oktoban 2024.
Theo Agada, mai fafutukar siyasa, ya bukaci shugaban da ya sauke Musawa saboda ya na ganin babu abin da ta tsinana.
A cewar Agada:
"Gaba daya Musawa ta gaza.”
Wacece Hannatu Musawa?
Hannatu Musawa lauya ce, ’yar siyasa kuma marubuciya da ke rike da mukamin ministar al’adu da kirkire-kirkire tun 2023.
Ta fito daga jihar Katsina a arewacin Najeriya kuma mahaifinta Marigayi Musa Musawa tsohon 'dan siyasa ne a yankin.
Musawa ta dade tana cikin harkokin siyasa a Najeriya, baya ga niyyar zama 'yar majalisa a 2011 a CPC, 'yar gwagwarmaya ce.
Ta kasance lauya a bangaren masu kara a karar zaben shugaban kasa na 2003 tsakanin Muhammadu Buhari da Olusegun Obasanjo.
Kokarin Hannatu Musawa a minista
A gefe guda kuma, Musawa ta bayyana cewa ma’aikatarta ta jawo jarin da ya kai dala miliyan 300.
Musawa ta bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Juma’a, 16 ga Mayun 2025, a Abuja.
Ta ce gwamnatin Tinubu na da burin samar da ayyuka miliyan biyu a bangaren kirkire-kirkire kafin 2027.
Ministar ta kara da cewa shugaban kasa zai kaddamar da cibiyoyin kirkire-kirkire a kowane yanki shida na Najeriya nan ba da jimawa ba.
An samu matsala kan sabon nadin Tinubu
Kun ji cewa wata kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta caccaki masu shirin zanga-zanga kan rashin goyon bayan nadin Cyril Tsenyil a NCDC.
Shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga ya ce wadanda ke adawa da nadin ba 'yan yankin ba ne, kuma suna aiki ne da jam’iyyar adawa.
Kungiyar matasa daga Plateau ta bukaci a janye nadin shugaban saboda zargin cewa ba ya wakiltar muradun jama’ar jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng