Katsina: Fusatattun Matasa Sun Cinnawa Fadar Basarake Wuta, An Yi Asara
- Matasa a garin Tsiga a jihar Katsina sun kone fadar dagacin garin bayan wani barawo ya nemi mafaka a can bayan ya daba wa mai babur wuka
- Jama’a sun bukaci a mika musu barawon amma aka hana, lamarin da ya tayar da hankali har ya kai ga kona fadar sarautar da ke Tsiga
- Wanda aka daba wa wuka yanzu yana cikin mawuyacin hali, yayin da lamarin ke kara tayar da kura a yankin karamar hukumar Bakori a Katsina
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bakori, Katsina - An shiga tashin hankali a garin Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.
An ce wasu fusatattun matasa sun cinna wuta a fadar dagacin Tsiga da ke karamar hukumar bayan biyo wani barawo.

Asali: Original
Katsina: Dalilin cinna wuta a fadar basarake
Shafin Bakatsine da ke kawo rahoto kan tsaro shi ya tabbatar da haka a dandalin X a jiya Talata 13 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce matasan sun cinna wa fadar dagacin Tsiga wuta, bayan wani barawo da ya daba wa mai babur wuka ya tsere ya buya a can.
Jama’an gari sun bukaci a mika musu barawon, amma aka ki yarda wanda hakan ya jawo tashin hankali a tsakanin al’umma.
“Wanda aka daba wa wukar yana cikin mawuyacin hali yanzu."
- Cewar wani mazaunin yankin

Asali: Facebook
Asarar da aka tafka a Katsina
Wasu rahotanni sun tattabar da cewa an samu asarar dukiyoyi sanadin haka wanda ya girgiza karamar hukumar Bakori.
Sanarwar ta ce:
"Fusatattun matasa sun kona fadar Dagacin Tsiga bayan wani barawo da ya daba wa wani direban babur wuka ya nemi mafaka a can.
"Jama’a sun bukaci a mika musu barawon, amma aka ki amincewa da hakan, lamarin da ya tayar da husuma a cikin garin.
"Wanda aka daba wa wukar yanzu yana cikin mawuyacin hali a asibiti, yana samun kulawa daga likitoci domin ceton rayuwarsa.
"Garin Tsiga na karkashin karamar hukumar Bakori a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya."
Karanta wasu labari da suka shafi Katsina:
- "Dogaran Sarki Sun Yi Ɓarna": Yadda Aka Yi Rikici a Wurin Bikin Auren Ɗiyar Gwamna Dikko
- 'Yan Bindiga Sun Zo Kwatar Abokinsu, Sojoji Sun Hallaka Hatsabibin Ɗan Ta'adda
- Dakarun Sojoji Sun Gwabza da 'Yan Ta'adda a Katsina, an Samu Asarar Rayuka
- Nazari: Ziyarar Tinubu a Jihar Katsina da Ra'ayin 'Yan Arewa gabanin Zaben 2027
An kona fadar babban Sarki a Edo
A baya, mun ba ku labarin cewa wasu fusatattun matasa sun kona fadar babban basaraken jihar Edo, Olojah na Ojah, Oba Okogbe Lawani.
Lamarin ya haifar da hatsaniya da tashin hankali a tsakanin mazauna garin Ojah da ke karamar hukumar Akoko-Edo a jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.
An tabbatar da cewa rikicin ya samo asali ne a yayin birne wata mata da ake zargin ta mutu a cikin gidan tsafi a yankin wanda ya ɗaga hankulan mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng