'An Bincike Su': Ƴan Sanda Sun Yi Ƙarin Haske da Aka Ga Baƙin Hausawa 89 a Titin Lagos

'An Bincike Su': Ƴan Sanda Sun Yi Ƙarin Haske da Aka Ga Baƙin Hausawa 89 a Titin Lagos

  • Rundunar ‘yan sandan Lagos ta ce wasu matasa da suka iso daga Katsina za su yi aiki ne a matatar Aliko Dangote da ke Ibeju-Lekki
  • Jami’an tsaro sun binciki samarin 89 da suka iso, an tabbatar da takardunsu da shaidarsu, kuma ba a samu wani abin da ya saba doka ba
  • Kwamishinan ‘yan sanda ya bukaci jama’a su daina yada bidiyon da ba a tabbatar da sahihancinsa ba domin gujewa tayar da hankali a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta yi karin haske kan bidiyon wasu Hausawa da aka gani a bakin titin Lagos.

Rundunar yan sanda ta mayar da martani kan bidiyon da ke yawo wanda ya tayar da hankula duba da abin da ya faru a jihar Edo.

Yan sanda sun wanke Hausawa da suka dura a Lagos
Yan sanda sun yi ƙarin haske da ake yada bidiyon Hausawa 89 a Lagos. Hoto: CSP Benjamin Hundeyin.
Asali: Twitter

Lagos: An yaɗa bidiyon da ake zargin Hausawa

Mai magana da yawun rundunar a Lagos, Benjamin Hundeyin shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook a yau Juma'a 16 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan yada faifan bidiyo wanda ya dauki hankulan al'umma da ake tunanin yan ta'adda ne suka dura a jihar daga Katsina.

Domin kwantarwa al'umma hankali, yan sanda sun yi gaggawar bincike da tabbatar da su a matsayin leburori da suka zo aiki a matatar Aliko Dangote.

Rundunar ta tabbatar da cewa an yi bincike kan matasan da aka gani da dama a Ibeju-Lekki a bidiyo da shafin Linderikejiblog ya wallafa.

Binciken farko ya nuna cewa matasan 89 sun fito daga jihar Katsina, kuma an dauke su aiki a matsayin ma’aikata a matatar Dangote da ke Lekki.

Rundunar ta ce bayan samun rahoto a ranar 14 ga Mayu 2025, ta tura jami’anta domin tabbatar da gaskiyar lamarin da ke cikin bidiyon.

Wani dan kwangila da ke aiki da matatar ya bayyana ga ‘yan sanda, ya kuma tabbatar da cewa shi ne ya dauko matasan Hausawa daga Katsina.

Yan sanda sun magantu bayan ganin Hausawa 89 a Lagos
Yan sanda yi bincike kan Hausawa 89 da aka gani a Lagos. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Binciken da 'yan sanda suka yi a Lagos

Babban jami’in tsaron matatar Dangote ya tabbatar da hakan, ya ce matasan sun samu sahalewa da kuma izinin shiga wajen aiki da zama.

An yi musu cikakken bincike, kuma babu wani abu da ya sabawa doka da aka samu tare da su, sun kuma nuna lambobin shaidarsu ta NIN.

Kwamishinan ‘yan sanda, Olohundare Jimoh ya bukaci jama’a su zauna lafiya, su guji yada labaran da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.

Ya kara da cewa rundunar ta himmatu wajen tabbatar da tsaro a Lagos, kuma za ta ci gaba da gaggauta daukar mataki kan duk wata barazana.

Edo: Iyalan mafarautan Kano sun yi zanga-zanga

Mun ba ku labarin cewa iyalan mafarautan da aka kashe a Edo sun gudanar da addu’a da zanga-zangar lumana a Kibiya da ke jihar Kano.

Mutanen sun koka da rashin sahihin bayani daga gwamnati, inda suka bukaci a tabbatar da adalci da cika alkawuran diyya da aka yi.

Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kibiya, Nasiru Adam Abdulaziz ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta Edo da su cika alkawari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.