"Ba sai Mun Jira FAAC ba": Gwamna Dauda Ya Fadi Shirin Daina Dogaro da Kudin Asusun Tarayya

"Ba sai Mun Jira FAAC ba": Gwamna Dauda Ya Fadi Shirin Daina Dogaro da Kudin Asusun Tarayya

  • Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya yi ƙarin haske kan yadda ɓangaren ma'adanai na jihar ke tafiya
  • Alhaji Dauda Lawal ya bayyana cewa jihar Zamfara ba ta samun ko sisin kwabo daga fannin a halin yanzu
  • Sai dai, ya nuna shirinsa na bunƙasa fannin ta yadda jihar za ta riƙa samun kuɗin shiga masu kauri don yin ayyukanta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi magana kan albarkatun ƙasan da jihar take da su.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda jihar, duk da yawan albarkatun ƙasa da take da su, ba ta samun ko sisin kwabo daga fannin a halin yanzu.

Dauda Lawal
Gwamna Dauda ya ce Zamfara ba ta samun ko kwabo daga fannin ma'adanai Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Dauda Lawal ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a ranar Laraba, 14 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dauda ya yi farin cikin dawo da haƙar ma'adanai

Sai dai ya nuna farin cikinsa da cewa soke haramcin da gwamnatin tarayya ta yi a kan haƙo ma'adanai ya ba shi damar fara tattaunawa da masu saka hannun jari da za su taimaka wajen raya wannan fannin da kuma ƙara kuɗaɗen shiga na jihar.

"Ina matuƙar farin ciki yanzu da gwamnatin tarayya ta janye takunkumin da ta sanya a kan haƙo ma’adanai. Idan ka lura, a bara cikin watan da ya gabata mun yi taro da wasu ƴan kasuwa masu zaman kansu da ke da hannun jari a jihar Zamfara."
“Wannan shi ne abin da mu ke ƙoƙarin yi yanzu, kawo masu saka hannun jari daga ɓangaren masu zaman kansu domin su saka jari a fannin ma’adanai, tare da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya."
"Idan hakan ya yi nasara, hakan na nufin ƙarin kuɗin shiga ga jihar Zamfara da kuma gwamnatin tarayya."

“Amma a halin yanzu da na ke magana, babu ko kwabo guda da jihar Zamfara ke samu daga fannin ma’adanai, abin takaici ne."

- Gwamna Dauda Lawal

Shirin Gwamna Dauda kan daina dogaro da FAAC

Gwamnan ya nuna kyakkyawan fatan cewa da zarar saka hannun jarin ya fara haifar da ɗa mai ido a fannin ma’adanai, jihar Zamfara ba za ta sake dogaro da kuɗaɗen da take samu daga asusun gwamnatin tarayya (FAAC) ba domin biyan buƙatunta.

Dauda Lawal
Gwamna Dauda ya ce Zamfara ba ta samun ko sisi daga fannin ma'adanai Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook
“A halin yanzu, daga cikin abubuwan da nake mayar da hankali a kai ƙarƙashin gwamnatina shi ne kallon wannan batu gaba ɗaya, da kuma farawa da kafa tsarin da ya dace domin jawo masu saka hannun jari cikin jihar da za su zuba jari a fannin ma’adanai."
"Da zarar mun aiwatar da hakan, bana tunanin Zamfara za ta ci gaba da dogaro da FAAC ba, za mu samu wadataccen kuɗin shiga wanda zai ba mu damar inganta jihar Zamfara wajen kawo ci gaba."

- Gwamna Dauda Lawal

Dauda Lawal ya taɓo batun sulhu da ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta hau teburin sulhu da masu laifi ba.

Gwamna Dauda ya nuna cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ƴan bindiga ba amma za ta karɓi waɗanda suka ajiye makamansu don ƙashin kansu.

Hakazalika ya bayyana cewa an samu ingantuwar harkokin tsaro a jihar saboda wasu matakai da gwamnatinsa ta ɗauka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng