"Kasa da N5m": Gwamna Ya Tona Asiri, An Ji Nawa Matawalle Ya Bari a Asusun Zamfara

"Kasa da N5m": Gwamna Ya Tona Asiri, An Ji Nawa Matawalle Ya Bari a Asusun Zamfara

  • Gwamna Dauda Lawal ya ce ya tarar da Naira miliyan 4 ne kacal a asusun gwamnatin jihar Zamfara lokacin da ya hau mulki a 2023
  • Ya bayyana cewa gwamnatin da ya gada ta bar bashin albashi, bashin wuta da bashi na WAEC da NECO da ya gagari dalibai jarrabawa
  • Dauda ya ce yanzu IGR na jihar ya karu daga Naira miliyan 90 zuwa sama da biliyan 2, wanda ya taimaka wajen biyan basussuka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamna Dauda Lawal ya bayyana irin halin matsin tattalin arziki da ya tarar da shi a jihar Zamfara lokacin da ya hau mulki a watan Mayu, 2023.

Gwamnan ya ce ya tarar da Naira miliyan hudu ne kacal a asusun gwamnatin jihar lokacin da ya karbi mulki, kuma ya gabatar da takardu da ke tabbatar da hakan.

Gwamnan Zamfara ya fadi halin da ya samu jihar bayan da ya hau mulki a 2023
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal. Hoto: @daudalawal
Asali: Twitter

"N4m kadai na gada" - Gwamnan Zamfara

Dauda Lawal ya yi wannan sabuwar bankadar ne a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Siyasa a Yau' na Channels TV a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Naira miliyan hudu aka bar masa sabanin ikirarin tsohon gwamna Bello Matawalle, wanda yanzu karamin ministan tsaron ne, da ke cewa ya bar miliyoyin kudi a asusun.

Gwamnan ya ce rashin kudi a asusun ya kasance babban kalubale ga gwamnatinsa, wanda ya tilasta shi karbo bashi domin biyan bukatun jihar na gaggawa.

Ya kara da cewa Matawalle ya bar jihar da matsaloli masu yawa, ciki har da bashin albashi, katsewar wutar lantarki, da gurguntar da tsarin ilimi.

A cikin matsalolin da ya gada, akwai bashin Naira biliyan 1.6 na WAEC da Naira biliyan 1.4 na NECO, wanda ya ce ya hana daliban jihar rubuta jarabawa na tsawon shekaru biyu.

Matsalolin Zamfara da Dauda ya ce ya tarar

Gwamnan ya bayyana cewa ya cimma matsaya da hukumomin jarabawar, inda ya biya bashin domin ba dalibai damar rubuta jarrabawar da kuma karbar takardunsu.

Dauda Lawal ya ce:

“Lokacin da na hau mulki, abin da na tarar a asusun gwamnatin Zamfara bai wuce Naira miliyan 4 ba. Gaskiya ce kuma akwai takardar da ke nuna inda aka bar wannan kudin. Sai na ce, wannan shi ne jagoranci; to me ya kamata mu yi?”

A fannin kudin shiga, Gwamna Dauda Lawal ya ce ya tarar jihar na tara Naira miliyan 90 na IGR a kowane wata, inda kaso 90 ke fitowa daga harajin PAYE.

Gwamna Dauda ya ce:

“Game da IGR, lokacin da na hau mulki, kudin shiga na jihar Zamfara ya tsaya ne a Naira miliyan 90. Amma ka san me? Kashi 90 cikin 100 daga ciki PAYE ne. Amma yanzu labari ya canza. Zan iya cewa muna samun fiye da Naira biliyan 2 a wata.”

Gamna Dauda Lawal ya fadi mawuyacin halin da ya samu jihar Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal. Hoto: @daudalawal
Asali: Facebook

Dauda ya karyata ikirarin Matawalle na barin N14m

A cewarsa, wannan ci gaban ya bai wa gwamnatinsa damar biyan bashin albashi na watanni hudu da suka wuce, da kuma biyan Naira biliyan 16.5 na fansho da ba a biya ba tun 2011.

Gwamnan ya karyata ikirarin Matawalle na cewa ya bar Naira biliyan 14, yana kalubalantar masu sukar sa da su fito da hujjoji.

Hakazalika, ya ce:
“Ni ba wani ba ne illa masanin aikin banki. Idan suna da hujja daban da tawa, su fito da ita. Ina mamakin inda wannan Naira biliyan 14 da suke magana a kai ta fito.
“Idan suna da irin wadannan makudan kudade, me ya hana su biyan WAEC da NECO? Me ya hana su biyan wuta? Lokacin da na hau mulki, gidan gwamnati ma ba shi da wuta."

- Gwamna Dauda.

'Halin da na samu jihar Zamfara' - Dauda

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana matsaloli da ci gaban da gwamnatinsa ta fuskanta tun bayan da ya fara mulkin jihar.

Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa ta gaji ɗumbin basussuka daga wajen gwamnatin Bello Matawalle wanda yanzu yake rike da mukamin karamin minista.

Ya bayyana cewa rashin tsaro ya yi katutu, tsarin ilimi ya rushe, ɓangaren kiwon lafiya mara kyau, da kuma ɗumbin basussuka da aka biyo jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.