Gwamna Uba Sani Ya Kafa Sabon Tarihi, Ya Samar da Masana'anta Ta Farko a Najeriya
- Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kafa tarihi a fannin haƙar ma'adanai na Najeriya ta hanyar kafa sabuwar masana'anta
- Uba Sani ya kafa masana'antar sarrafa lithium wacce ita ce ta farko a Najeriya, kamfanin ya na ƙauyen Kangimi da ke jihar Kaduna
- Kwamishinan muhalli da albarkatun ƙasa wanda ya bayyana hakan ya ƙara da cewa jihar ta samu kuɗin shiga daga haƙar ma'adanai a 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya kafa masana'antar sarrafa lithium ta farko a Najeriya a ƙauyen Kangimi, da ke kan hanyar Kaduna zuwa Jos.
Masana'antar da Gwamna Uba Sani ya kafa na da ƙarfin samar da fiye da tan 30,000 na lithium a kowace rana.

Asali: Twitter
Jaridar The Nation ta ce wannan bayanin ya fito ne daga bakin kwamishinan muhalli da albarkatun ƙasa, Alhaji Abubakar Buba, yayin taron manema labarai na ma'aikatu da ake gudanarwa a kowane wata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihar Kaduna na da albarkatun ƙasa
Alhaji Abubakar Buba ya bayyana jihar Kaduna a matsayin cibiyar albarkatun ƙasa a Najeriya, inda ya ce jihar na da fiye da nau’in albarkatun ƙasa 70, ciki har da lithium, zinare, ƙarfe (tin), coltan, wolframite, titanium da iron.
Ya ce Gwamna Uba Sani yana da ƙudurin sake fasalta fannin albarkatun ƙasa domin bunƙasa samun kuɗaɗen shiga na cikin gida, jawo masu zuba hannun jari daga waje, ƙirƙirar ayyukan yi, da kuma daƙile haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a jihar.
A cikin wannan yunƙuri, gwamnatin jihar ta haɗa kai da kamfanin Core International Marketing and Management Ltd domin haɓaka ci gaban haƙar ma’adanai a jihar Kaduna.
A cewar Buba, jihar ta samu Naira miliyan 30 daga ayyukan haƙar ma’adanai a watanni shidan ƙarshe na 2024, tare da hasashen samun ƙarin kuɗi a shekarar 2025, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
Gwamna Uba Sani ya kafa tarihi
"Mai girma Gwamna Uba Sani ya kafa masana’antar sarrafa lithium a ƙauyen Kangimi da ke kan hanyar Kaduna zuwa Jos, wadda ita ce ta farko irinta a Najeriya."
“Wannan masana’anta na da ƙarfin sarrafa fiye da tan 30,000 na lithium a kowace rana."
- Alhaji Abubakar Buba

Asali: Facebook
Kwamishinan ya ƙara da cewa an samu ci gaba sosai waje rage ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a jihar Kaduna.
Ya ce hakan ya samu ne sakamakon ƙarfafa bincike da sa ido, tare da sababbin dabaru da Gwamna Uba Sani ya ɓullo da su.
Me kuka sani game da lithium?
Lithium wani muhimmin sinadari ne wanda ake amfani da shi sosai a masana’antar zamani, musamman wajen kera batir na na’urorin lantarki kamar wayoyin hannu, kwamfutoci, da kuma motocin lantarki.
Hakanan lithium na da matukar amfani wajen samar da makamashin sabbin hanyoyin ajiya, wanda zai taimaka wajen rage dogaro ga man fetur da makamashin gargajiya.
A Najeriya, kafa masana’antar sarrafa lithium ta farko a Kaduna babban ci gaba ne da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa.
Hakan zai sa Najeriya ta kasance cikin kasashen da ke taka rawar gani a fannin samar da lithium a duniya, musamman ma a lokacin da duniya ke kara bukatar makamashi mai tsafta da kuma sabbin fasahohi.
Masana’antar lithium za ta kawo ribar tattalin arziki ta hanyoyi da dama, ciki har da habaka fannin masana’antu, kawo jari daga kasashen waje, da kuma bunkasa fasahar kere-kere a kasar.
Bugu da kari, hakan zai rage shigo da kayayyaki daga waje, wanda ke rage asarar kudaden kasashen waje.
Wannan mataki na jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani zai taimaka wajen sauya tattalin arzikin Najeriya zuwa sabon yanayi na ci gaba da dorewa.
Uba Sani ya koka kan ta'ammali da ƙwayoyi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya nuna damuwa kan yadda matasa ke ta'ammali da ƙwayoyi a Arewacin Najeriya.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa matsalar ta zama ruwan dare a yankin Arewa maso Yamma inda alƙaluma suka nuna mutum ɗaya cikin bakwai yana ta'ammali da ƙwaya.
Hakazalika gwamnan ya bayyana cewa hakan ba ƙaramar gagarumar matsala ba ce ga tsaro da zaman lafiya a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng