'Kisan Sojoji a Borno': An Sake Matsawa Tinubu, Ana So Dole Ya Tsige Ministan Tsaro

'Kisan Sojoji a Borno': An Sake Matsawa Tinubu, Ana So Dole Ya Tsige Ministan Tsaro

  • Wata kungiya ta nemi Shugaba Bola Tinubu da ya sallami ministan tsaro saboda gazawarsa wajen magance matsalar tsaro a Najeriya
  • Kungiyar ta nuna ɓacin rai game da yawaitar hare-haren 'yan ta'adda a kasar ba tare da Mohammed Badaru ya dauki wani mataki ba
  • Amina Mohammed ta bukaci Tinubu da ya kori Badaru, ya naɗa ƙwararre don daidaita rundunonin soji da ƙarfafa yaƙi da ta'addanci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata ƙungiyar masu rajin kare gaskiya da riƙon amana, ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sallami ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, nan take.

Ƙungiyar, Ethics Vanguard, ta bukaci Tinubu da ya kori Badaru saboda abin da suka kira 'rashin ƙwarewa wajen magance matsalar tsaro da ke ƙara ta'azzara a Najeriya'.

Kungiyar Ethics Vanguard ta nemi Tinubu ya tsige ministan tsaro
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

An nemi Tinubu ya sallami ministan tsaro

A cikin wata sanarwa da suka fitar jiya a Abuja, ƙungiyar ta nuna ɓacin rai game da ƙara tabarbarewar tsaro a kan idon Badaru, kamar yadda jaridar ThisDay ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ta yi ƙorafi game da yadda ake kashe 'yan Najeriya ba dare ba rana ta hanyar hare-haren 'yan ta'adda, 'yan fashi, masu garkuwa da mutane, da sauransu.

A cewar shugabar kungiyar, Miss Amina Mohammed, lokaci ya yi da za a ɗauki mataki mai ƙarfi, ba wai a rika daukar alkawuran da ba za a cika ba.

Miss Amina ta nace cewa dole ne Shugaba Tinubu ya maye gurbin Badaru da ƙwararre a dabarun tsaro, wanda zai iya daidaita rundunonin soji tare da ƙarfafa ayyukan yaƙi da ta'addanci na Najeriya.

An soki Badaru kan gaza magance matsalar tsaro

Ta bayyana cewa:

"Yawan hare-hare a faɗin Najeriya a kan idon Mohammed Badaru Abubakar a matsayin ministan tsaro abin tsoro ne, kuma ba za mu amince da hakan ba.

Ta ƙara da cewa:

"Daga Plateau zuwa Kudancin Kaduna, Benue, Zamfara, Sokoto, har ma da Abuja, ana yanka 'yan Najeriya kamar dabbobi a gidajensu, gonakinsu, makarantunsu da manyan hanyoyi.
"Maimakon mu ga ministan tsaro a kan gaba wajen shawo kan matsalolin nan, sai muka ga ya koma baya ya yi shiru, ya tsaya a iya ofis dinsa ba tare da katabus ba."

Ƙungiyar Ethics Vanguard ta bayyana naɗin Badaru a matsayin misali ne na gazawa wajen dora wadanda suka dace a muhimman mukamai a kasar nan.

Kungiyar EV ta shaida wa Tinubu cewa Badaru ba shi da kwarewar magance matsalar tsaro
Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar. Hoto: @Mohammed_Badaru
Asali: Facebook

"Badaru ba shi da kwarewa" - Miss Amina

Ya jaddada cewa bai kama shugaban kasa ya dauki mukamin ministan tsaro na Najeriya ya bai wa mutumin da ko a tarihin aikinsa bai cancanci mukamin ba.

"Abin takaici ne matuƙa cewa a lokacin da ƙasar Najeriya ke fuskantar yaƙi mai tsanani daga 'yan tawaye da 'yan ta'adda, ministan tsaro, ya kasa yin katabus wajen daukar mataki.

"A bayyane yake Badaru na amfani da hanyoyin da suka tsufa a fuskantar yaƙi da 'yan ta'adda. Wannan ministan ba shi da ƙwarewar dabarun yaki, ba shi da horon aiki, ba shi da hangen nesa."

- Miss Amina Mohammed.

Wannan kiran na zuwa ne yayin da 'yan ta'addan da ake zargin Boko Haram ne suka sake farmakar sansanin sojoji a Borno, inda suka kashe wasu, suka kama wasu, tare da kwashe makamai.

Kungiyar AYPN ta nemi a tsige Badaru

Tun da fari, mun ruwaito cewa, kungiyar matasan Yarbawa (AYPN), ta nemi Shugaba Bola Tinubu da ya kori ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar.

Kungiyar AYPN ta ce ƙara tabarbarewar tsaro a sassan Najeriya ta kai intiha, don haka dole ne Tinubu ya gaggauta sallamar Mohammed Badaru.

Matasan Yarabawa sun zargi Badaru da fifita muradun kansa a kan tsaron 'yan Najeriya, tare da zargin aikata ba daidai ba a ma'aikatar tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.