'Ka Zubar Mana da Mutunci': An Soki Sarkin Hausawa da Gwamna Ya ba Shi Muƙami
- Matasan Arewa a Enugu sun soki Sarkin Hausawan jihar, Yusuf Sambo II, bisa amincewa da mukamin hadimin gwamna na musamman
- Shugaban kungiyar, Hamza Buba Ganye, ya ce wannan mataki ya ci karo da darajar masarauta, yana kuma iya raunana wakilcin al’umma
- Ganye ya bukaci shugabannin Arewa su shiga tsakani, yana cewa hakan na iya zama hanyar danne ‘yan Arewa da haifar da rikici siyasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Enugu - Sarkin Hausawa a jihar Enugu ya jawo fushin al'ummarsa bayan tsoma kansa a lamuran gwamnati.
Wasu matasa da ke zaune a jihar sun caccaki basaraken bayan karban muƙamin a gwamnatin Peter Mbah saboda rashin daraja sarautar gargajiya.

Asali: Twitter
'Yan Arewa sun soki Sarkin Hausawan Enugu
Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar matasan, Hamza Buba Ganye ya bayyana a yau Laraba 14 ga watan Mayun 2025, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun ce Matasan Arewa a jihar sun soki Sarkin, Yusuf Sambo II, bisa karɓar mukamin hadimi na musamman ga gwamnan jihar Enugu.
Ganye ya kira matakin da Sarkin ya dauka na karbar muƙamin a ranar 2 ga Mayun 2025 a matsayin koma baya.
Ya ce:
“Nadinsa yana raunana ikon gargajiya da ‘yancin majalisar masarauta. "Wannan yana ba da saƙo mara kyau ga al’umma kuma yana cutar da wakilcinsa.”

Asali: Original
Hausawa sun nuna damuwa kan muƙamin Sarki
Ganye ya nuna bakin ciki da cewa Sarkin ya karɓi mukamin siyasa da zai iya lalata mutunci da ikon al’adar gargajiya da masarautarsa.
Ya ƙara da cewa:
“Mun yi tsammani shugabanninmu za su fi haka. Cece-kuce game da nadin ya tayar da muhawara mai zafi a cikin al’umma.
“A yayin da lamarin ke cigaba, abu guda ya tabbata: Wannan nadin zai haifar da tasiri mai fadi a nan gaba."
Ganye ya roƙi Kungiyar Tsofaffin Shugabannin Arewa, Kungiyar Hadin Kan Matasa Arewa da sauran shugabanni su shiga tsakani da gaggawa.
Ya bayyana lamarin a matsayin yunkuri na danniya da kokarin girka tasirin siyasa a cikin al’ummar Hausawa da ke Enugu.
Karanta wasu labarai kan sarakunan Hausawa:
- Olubadan Ya Gargadi Fitaccen Sarkin Hausawa na Sasa kan Ikirarin Iko a Yankin
- An Warware Rawanin Sarkin Hausawa, Haruna Maiyasin Bisa Zargin ya Raina Sarkin Yarbawa Olubadan
- Majalisar Sarakunan Arewa Sun Goyi Bayan Sarkin Hausawa da Aka Dakatar Kan Raina Olubadan Na Ibadan
- 'Mun Yi Babban Rashi': Gwamna Ya Girgiza da Mutuwar Sarkin Hausawa, Haruna Maiyasin
Sarkin Hausawa a jihohin Kudu ya rasu
A baya, kun ji cewa Allah ya yi wa Sarkin Sasa da ke Ibadan a jihar Oyo, Alhaji Haruna Maiyasin rasuwa bayan ya shafe shekaru da dama kan karagar mulki.
Marigayin kafin rasuwarsa, shi ne ke riƙe da muƙamin Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a jihohi 17 na Kudancin Najeriya gaba daya.
Majiyoyi sun ce an yi sallar jana'izarsa a ranar Lahadi 2 ga watan Maris din shekarar 2025 yayin da Sarakunan Hausawa da malaman addini suka halarta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng