Mataimakin Gwamna Ya Gamu da Hatsarin Mota a Najeriya, An Ji Halin da Yake Ciki

Mataimakin Gwamna Ya Gamu da Hatsarin Mota a Najeriya, An Ji Halin da Yake Ciki

  • Motocin ayarin mataimakin gwamnan jihar Cross River, Peter Odey, sun gamu da hatsari a kan hanyar Ikom zuwa Kalaba
  • Hatsarin ya faru ne kusa da Ugep da ke a karamar hukumar Yakurr, kuma mutane da dama daga cikin hadimansa sun ji raunuka
  • Rahotanni sun nuna cewa mataimakin gwamnan ya tsallake rijiya da baya, amma wasu daga cikin motocin ayarin sun lalace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River, Nigeria - Motocin ayarin mataimakin gwamnan jihar Cross River, Dr Peter Odey, sun yi hatsari a ranar Lahadi a kan hanyar Ikom-Calabar, kusa da Ugep, hedikwatar karamar hukumar Yakurr ta jihar.

Hatsarin ya faru ne yayin da mataimakin gwamnan da wasu mambobin tawagarsa ke komawa Kalaba, babban birnin jihar daga karamar hukumar Obanliku, inda suka halarci wani taron aiki na gwamnati.

Kara karanta wannan

Kwanaki 10 kafin a fara kamfen, sabani ya shiga tsakanin Atiku da ADC

Dr Peter Odey.
Mataimakin gwamnan jihar Cross River, Dr Peter Odey a ofishinsa a gidan gwamnati da ke Kalaba Hoto: Solomon Abang
Source: Facebook

Yadda hatsarin ya faru a Cross River

Sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Fred Abua, ya tabbatar wa jaridar Vanguard faruwar hatsarin.

Ya ce motar ma’aikatan yada labarai da wata motar Hilux da ke cikin ayarin ne hatsarin ya shafa.

A cewar Abua, birkin motar ma’aikatan yada labarai nd ya samu matsala ne, lamarin da ya tilasta wa direban karkatar da motar daga kan hanya.

Ya ce motar da ke dauke da mataimakin gwamnan ba ta shiga hatsarin kai tsaye ba, kuma Odey bai ji rauni ba.

Abua ya ce:

“Motar ma’aikatan yada labarai da Hilux ne kawai hatsarin ya shafa. Birkin motar ma’aikatan yada labarai ya samu matsala, sai direban ya karkata daga kan hanya.”

Wasu hadimai sun samu raunuka

Sai dai rahotanni sun nuna cewa wasu hadiman mataimakin gwamnan da ke cikin ayarin sun samu raunuka sakamakon hatsarin.

Wata majiya ta ce motar manema labarai ta fadar gwamnatix wadda ke dauke da wasu wadanda aka nada mukamai da ma’aikatan ofishin mataimakin gwamnan, ta sauka daga kan hannunta ta kusa da wani shingen binciken sojoji a Ugep.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta sake girgiza Najeriya, tsohon antoni janar ya riga mu gidan gaskiya

Majiyar ta ce motar ta bugi shingen da aka yi da buhunan yashi kafin ta tsaya.

Ita ma wata majiyar ta danganta hatsarin da matsalar birki, tare da cewa wasu motocin ayarin sun samu barna.

Cross River.
Taswirar jihar Cross River da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wasu motoci sun samu matsala

Har zuwa lokacin hada rahoton, ba a iya tantance girman raunin da wasu mutane da ke ayarin suka samu ko kuma adadin barnar da motocin suka yi ba.

Haka kuma, kokarin tuntubar wasu jami’an gwamnati domin samun karin bayani kan hatsarin bai yi nasara ba, cewar rahoton Punch.

Lamarin ya faru ne yayin da mataimakin gwamnan da tawagarsa ke dawowa daga wata ziyarar aiki a Obanliku, inda suke kan hanyar komawa babban birnin jihar, Calabar.

Dan Majalisa ya yi hatsari a Nasarawa

A wani rahoton, kun ji cewa hatsarin mota ya rutsa da mataimakin kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Muhammad Adamu Oyanki a titin Keffi zuwa Akwanga.

Motar da ya ke ciki ta samu mummunar barna sakamakon hatsarin, inda daga bisani aka kwashe ta zuwa harabar Majalisar Dokoki da ke Lafia.

Kakakin Majalisar Dokokin Nasarawa, Rt. Hon. Dr. Danladi Jatau, tare da wasu ‘yan majalisa, sun kai ziyara domin duba motar da hatsarin yanrutsa da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262