Yadda Tinubu ke Tafiya da Kafa Zuwa Ofis da Rashin Cin Abinci saboda Aiki
- Shugaban Hukumar Tara Kuɗin Shiga ta Najeriya (NRS), Zacch Adedeji, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya rayuwa cikin almubazzaranci duk da matsayinsa
- Adedeji ya bayyana cewa Bola Tinubu kan yi tafiya da ƙafa daga gidansa zuwa ofis, kuma yana cin abinci sau ɗaya kacal a rana
- Ya fadi hakan ne yayin wata hira, inda ya mayar da martani kan zargin almubazzarancin jami'an gwamnati a lokacin da 'yan Najeriya ke fuskantar matsin tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaban Hukumar Tara Kuɗin Shiga ta Najeriya (NRS), Zacch Adedeji, ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan yadda manyan jami'an gwamnati ke gudanar da rayuwarsu a lokacin da ake fuskantar tsadar rayuwa.
Adedeji ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya rayuwa cikin alatu kamar yadda wasu ke zargi, yana mai cewa shugaban kan yi tafiya da ƙafa daga gidansa zuwa ofis.

Kara karanta wannan
Dalilin da ya sa NRS ke ganin cire tallafin man fetur shi ne mafi alheri ga 'yan Najeriya

Source: Twitter
Adedeji ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin ɗin Channels ranar Lahadi, inda aka tambaye shi game da yadda shugabannin siyasa ke rayuwa a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki.
Tinubu na zuwa ofis da ƙafa
Adedeji ya ce Tinubu ba ya amfani da mota wajen zuwa ofis daga gidansa, sai dai idan yana tafiya zuwa filin jirgin sama.
Ya kuma yi watsi da tambayar da aka yi masa kan yawan motocin alfarma irin su Escalade da ake zargin suna cikin ayarin shugaban ƙasar.
Ya ce shugaban ƙasa yana da ikon mallakar irin waɗannan motoci, don haka bai kamata a ɗauki amfani da su a matsayin abin kunya ba.
Punch ta rahoto ya ce:
“Shugaban ƙasa yana tafiya daga gida zuwa ofis da ƙafa, ba ya ma amfani da mota sai lokacin da zai je filin jirgin sama. Ban san inda kuke ganin wannan ayarin motoci ba. Kafin ya zama shugaban ƙasa, me yake hawa?
“Nawa ne farashin motar Escalade da shugaban Najeriya ba zai iya saya ba? Don Allah kada ku kunyatar da ƙasar nan.”
Tinubu na cin abinci sau 1
Shugaban NRS ɗin ya kuma yi ikirarin cewa Tinubu yana cin abinci sau ɗaya kacal a rana. Ya ce hakan na daga cikin abubuwan da yake ganin ya kamata a duba kafin a zargi shugaban da rayuwa cikin almubazzaranci.
Adedeji ya ce:
“Me ake nufi da rayuwa cikin almubazzaranci? A cikin watannin baya, bai ma fita daga Najeriya ba, yana tafiya da ƙafa kuma yana aiki. Idan ka je wurinsa yanzu, za ka same shi yana duba takardu.
“To me ake nufi da rayuwa cikin almubazzaranci? Shugaban ƙasa yana cin abinci sau ɗaya a rana. Sau nawa kuka gan shi a wurin bukukuwa cikin shekaru uku da suka gabata? Ku gaya mini inda kuka gan shi, ko yana hutu ko kuma a wani wuri.”

Source: Twitter
Maganar cire tallafin mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa Zacch Adedeji ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin mafi kyawun abu da ya taɓa faruwa da Najeriya.
Adedeji ya ce Shugaba Bola Tinubu ya cancanci yabo saboda ɗaukar matakin cire tallafin, yana mai cewa tsarin tallafin ya kasance ba mai ɗorewa.
Ya ce nasarorin tattalin arzikin da gwamnati ke samu sun samo asali ne daga matakin da Tinubu ya ɗauka na cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng

