Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sauke Kwandon Alheri a Jami'o'in Jihar 2

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sauke Kwandon Alheri a Jami'o'in Jihar 2

  • Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya waiwayi wasu daga cikin jami'o'in da ke jihar da karin albashi inda aka fitar masu da sabon tsari
  • Gwamnatin jihar za ta kashe sama da N391m duk wata wajen biyan sabon tsarin albashin ma’aikatan jami’o’in biyu saboda inganta rayuwarsu
  • Bayanin wannan sabon tsari na dauke a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yammacin Litinin 10 ga watan Agusta, 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da aiwatar da sabon tsarin sake duba albashin malaman jami’a da ma’aikatan da ba malamai..

Ma'aikatan da aka bullo wa da wannan tsari sun hada da na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil da Jami’ar Northwest da ke Kano.

Kara karanta wannan

Sakon Abba ga Malamai, Sarakuna da Gwamnonin da suka halarci auren gata a Kano

Gwamnatin Kano ta kara albashin ma'aikatan jami'o'i
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin 20 ga watan Agusta, 2026 kuma aka wallafa a shafin Facebook.

Abba ya kara albashin jami'o'i

Sanarwar ta ce sabon tsarin albashin an tsara shi ne bisa tsarin biyan albashin da gwamnatin tarayya ta aiwatar a jami’o’in gwamnatin tarayya da ke fadin Najeriya.

A cewar sanarwar, amincewar gwamnan ta biyo bayan rahoto da shawarwarin wani kwamiti da Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta kafa domin duba bukatar jami’o’in biyu na amfani da sabon tsarin albashin.

Sanarwar ta bayyana cewa sabon tsarin albashin zai fara aiki daga watan Janairun 2026, yayin da za a fara Dan kudin daga watan Satumban 2026.

Ta ce sabon tsarin zai jawo a kashe N391,847,555.24 duk wata, wanda zai kai N4,702,170,662.88 a shekara ga jami’o’in biyu.

Jami'ar Wudil za ta amfana

Dangane da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, gwamnatin jihar za ta kashe N228,195,210.83 duk wata wajen biyan sabon tsarin.

Kara karanta wannan

EFCC ta rufe asusun gwamnatin jiha sukutum, an jefa gwamna a matsala dab da zabe

Gwamnatin Kano ta fadi dalilin kara albashin
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Daga cikin wannan kudin, N141,082,223.37 za a kashe kan malaman jami’ar da ke karkashin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, yayin da N87,112,987.46 za a ware wa ma’aikatan da ba malamai ba karkashin SSANU.

A Jami’ar Northwest da ke Kano kuwa, gwamnatin jihar za ta kashe N163,652,344.41 duk wata. Wannan ya kunshi N112,238,985.30 ga malaman jami’ar da kuma N51,413,359.11 ga ma’aikatan da ba malamai ba.

Sanarwar ta kuma ce gwamnatin jihar ta amince da ware N1,567,390,220.96 a cikin karin kasafin kudin shekarar 2026 domin biyan sabon tsarin albashin daga watan Satumba zuwa Disamba.

Ta ce bashin karin albashin da ya kamata a biya daga watan Janairu zuwa Agustan 2026, wanda ya kai N3,134,780,441.92, za a sanya shi cikin kasafin kudin shekarar 2027.

A cewar sanarwar, an dauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya tsakanin gwamnati da kungiyoyin ma’aikata tare da inganta walwalar ma’aikatan jami’o’in biyu.

Kara karanta wannan

A ba su wuta: Gwamnan Bauchi ya umarci sojoji a shafe 'yan bindiga

Gini ya ruguje a Kano

A baya, kun samu labarin cewa kwana guda bayan faruwar lamarin, Ma’aikatar kashe gobara ta Kano ta ceto mutane 16 bayan wani ginin zama ya ruguje a Fagge inda ya jawo gagarumar asara.

Wasu mutane na ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin baraguzan ginin, yayin da jami’an ceto ke gudanar da aikin neman waɗanda suka makale kuma an ceto yara uku da ba su cikin hayyacinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an kashe gobara sun kai agajin gaggawa bayan sun samu kiran faruwar lamarin, inda suka ce ba a gano musabbabin rugujewar ginin ba har aka kammala aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng