Majalisa Ta Yi Fatali da Kudirin Karɓa Karɓa na Shugaban Kasa da Mataimakinsa

Majalisa Ta Yi Fatali da Kudirin Karɓa Karɓa na Shugaban Kasa da Mataimakinsa

  • Majalisar wakilai ta ƙi amincewa da kudurin dokar sauya kundin tsarin mulki da ke neman juyawa shugabanci tsakanin yankuna shida
  • Mambobin da dama sun ce tsarin karba-karba zai haifar da rikici da ƙabilanci inda suka ce ya kamata a bar shi kamar yadda yake
  • Wasu 'yan majalisa sun goyi bayan kudurin, suna cewa zai kawo adalci, sai dai kudurin bai samu amincewa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai ta yi zama game da kudirin karba-karba a yankunan Najeriya kan zaben shugaban kasa.

Majalisar ta ƙi amincewa da kudurin sauya kundin tsarin mulki da ke neman jujjuwa shugabancin ƙasa tsakanin yankuna shida.

Majalisa ta yi watsi da kudirin kan karba-karba
Majalisa ta ki amincewa da kudirin karɓa karɓa. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

Kudirin da aka tattauna a majalisa

Bugu da ƙari, majalisar ta ƙi wasu ƙudurorin sauya kundin mulki guda shida da aka jera domin yin nazari da yanke hukunci a kansu, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta yanke shawarar rushe dokarta domin ta ba da dama a tattauna dukkan kudurorin sauya kundin tsarin mulki a lokaci guda.

Yawancin 'yan majalisa sun zaɓi tattauna kan kudurin da ke neman karɓa-karɓa a shugabancin ƙasa, inda da dama suka nuna adawa da haka.

Jagoran marasa rinjaye, Aliyu Madaki, ya ce Hukumar Halayyar Ƙasa ta riga ta magance irin matsalolin da kudurin ke son gyarawa.

Madaki ya ƙara da cewa jam’iyyun siyasa suna da tsarin da ke tabbatar da wakilci bisa adalci a lokacin zaɓe a kowane lokaci.

Sada Soli (APC, Katsina) ya ce tunanin gyaran ba laifi ba ne, amma ya tambaya ko hakan ba zai cutar da ingancin shugabanci ba.

Majalisa ta tattauna kudirin karɓa-karɓa
Majalisa ta ki amincewa da kudirin karɓa-karɓa na shugaban kasa. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

Yadda 'yan majalisa suka tattauna kudirin

A nasa jawabi, Shina Oyedeji (PDP, Oyo) ya ce idan an saka tsarin a kundin mulki, kowace jiha da ƙabila za su fara neman adalci, cewar Sahara Reporters.

Ya ce:

“Idan kuka saka tsarin kuma ya zo Kudu maso Yamma, shin wace jiha za a ba? Ogun ko Oyo?”

Bello Mohammed El-Rufai ya tambayi abin da zai faru idan shugaban ƙasa ya rasu a ofis kamar yadda ya faru da Umaru Musa Yar’adua.

Ya ce saka wannan tsari a kundin zai hana 'yan Najeriya damar tsayawa takara, kuma har yanzu za a ci gaba da rashin amincewa da juna.

Amma Hon. Ali Isa daga Gombe ya ce ya kamata kowane yanki ya samu damar shugabanci, har ma a matakin gwamnoni a jihohi.

Ya ce kowanne yanki yana da masu cancanta da za su iya jagorantar Najeriya da ma yankin yammacin Afirka, bisa ka’idar adalci da halayya.

A nasa jawabi, Clement Jimbo (APC, Akwa Ibom) ya ce kudurin zai magance rashin adalcin da aka dade ana yi wa ƙananan ƙabilu.

Ya ce ya kamata a saka sharadi a cikin kundin da zai kawo ƙarshen tsarin bayan kowane yanki ya samu damar shugabanci.

Amma kudurin bai samu nasarar karatu na biyu ba bayan tattaunawa da kuri’ar murya da aka kada tsakanin 'yan majalisar.

'Dan majalisa ya koka kan ta'asar Boko Haram

Kun ji cewa dan majalisa daga Plateau, Hon. Yusuf Gagdi ya bayyana cewa Boko Haram sun kwace makaman sojoji da kudinsu ya kai tiriliyoyin Naira.

Hon. Gagdi ya ce Majalisa ta ware kuɗi masu yawa don sayen makamai da motocin yaƙi, amma ’yan ta’adda na ci gaba da kwace su.

Ya yi gargaɗi cewa idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, ’yan Najeriya za su iya ɗaukar matakin kare kansu da kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.