"Dalilan da Suka Sa Zaman Lafiya Ya Fara Dawowa Zamfara," Gwamna Ya Jero Abubuwa 3
- Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa tsaro ya fara inganta a jihar Zamfara sakamakon wasu matakai akalla uku da ya ɗauka
- Dauda Lawal ya ce daina sulhu da ƴan bindiga, kafa rundunar tsaro da tallafawa jami'an tsaro da kayan aiki sun taimakawa jihar
- Gwamnan ya ce a halin ƴanzu ƴan ta'adda sun rasa kwanciyar hankali saboda matsin lambar da suke fuskanta daga jami'an tsaro
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara wajen samar da tsaro a jihar.
Gwamna Lawal ya ce tsaro ya fara inganta a Zamfara sakamakon matakan da ya ɗauka na ƙin sulhu da ƴan bindiga, kafa rundunar tsaro da tallafawa jami’an tsaro da kayan aiki.

Asali: Facebook
Dauda Lawal ya bayyana hakan ne da yake bayani a shirin siyasa a yau na Channels TV a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wane hali Dauda Lawal ya karɓi Zamfara?
Gwamna Lawal ya ce ya karɓi mulki a lokacin da jihar ke cikin matsanancin halin rashin tsaro da rikice-rikice da suka dauki sama da shekaru goma.
Ya ce:
"Matsalar tsaro wani abu ne da muka zo muka tarar, ina hawa gadon mulki, ɗaya daga cikin abubuwa na farko da na yi shi ne kafa rundunar tsaron al'umma a faɗin ƙananan hukumomi 14."
"Mun zabi mutane bisa cikakken binciken sirri na DSS, an horar da su yadda za su zama garkuwa ta farko kafin isowar jami’an tsaro.”
Gwamna Lawal ya kafe kan batun sulhu
Gwamna Lawal ya kuma sake jaddada matsayarsa kan sulhu da ƴan bindiga wanda ya faɗa tun watan Fabrairu, ya ce ba maganar tattaunawa da miyagu.
A rahoton Daily Trust, gwamnan ya ce:
"Mun ki yin sulhu da ‘yan bindiga saboda ba na ganin hakan ce mafita. Sai dai duk wanda ke son mika wuya ba tare da sharadi ba, mu na maraba da shi amma ba da wata yarjejeniya ba."
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ware kuɗi masu tsoka wajen samar da kayan aiki da daukar nauyin ayyukan jami’an tsaro, kuma hakan ya fara tasiri.

Asali: Facebook
Nasarorin da aka samu a tsaron Zamfara
“Yanzu an daina jin labarin munanan hare-hare wanda zaka ji ance maharan sun kashe mutane 200 a rana. Duk da cewa akwai wuraren da har yanzu ake samun hare-hare, tsaron jihar Zamfara ya inganta matuka.
“Sau da dama muna kama motocin da ke shigo da makamai daga Fatakwal, Filato da Nasarawa. A halin yanzu ƴan ta'adda na cikin matsi, kwanan nan muka raba wa jami'an tsaro motocin aiki 140.
“Mun ba su motocin ne domin su samu saukin gudanar da ayyukansu da kuma tunkarar ‘yan bindiga a ko’ina cikin jihar Zamfara."
- Dauda Lawal.
Sai dai wasu mazauna Zamfara sun shaidawa Legit Hausa cewa ko da an samu sauƙi a wasu yankuna, to fa har yanzu babu kwanciyar hankali a garuruwa da dama.
Zayyanu Abdullahi ya koka kan halin da mutanen yankinsu a ƙaramar hukumar Zurmi ke ciki, yana mai kira ga jami'an tsaro su ƙara ƙaimi a yaƙi da ƴan ta'adda.
"Mu a nan garin Moriki da ke yankin Zurmi ba mu da kwanciyar hankali, mafi yawan mutane ba su iya kwana a gidajensu
"Muna kira za hukumomin tsaro da babban jami'in tsaro na Zamfara su taimaka a duba wannan lamarin," in ji shi.
Haka wani mai suna Ɗan Asabe ya shaida mana cewa bai kamata gwamna yana irin wannan magana ba, domin ƴan bindiga na nan suna cin karensu babu babbaka.
Gwamna Lawal ya faɗi kudin da ya tarar a asusu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Zamfara ya sake kokawa kan kuɗin da ya tarar a baitul malin jihar lokacin da ya karɓi mulki daga hannun Bello Matawalle.
Gwamna Dauda Lawal ya ce ya tarar da Naira miliyan hudu ne kacal a asusun gwamnatin jihar lokacin da ya karbi mulki a watan Mayu, 2025.
Gwamnan ya ce rashin kudi a asusun ya kasance babban kalubale ga gwamnatinsa, wanda ya tilasta shi karbo bashi domin biyan bukatun al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng