Bauchi: An Hallaka Ƴan Bindiga Fiye da 60, Gwamna Ya ba da Tallafin Maƙudan Kuɗi

Bauchi: An Hallaka Ƴan Bindiga Fiye da 60, Gwamna Ya ba da Tallafin Maƙudan Kuɗi

  • Gwamnan Bauchi ya tabbatar da mutuwar ‘yan bindiga fiye da 60 a harin da ya faru a kauyen Mansur a karamar hukumar Alkaleri
  • Bala Mohammed ya ce mutane 21 sun mutu ciki har da yan banga 13 da fararen hula takwas inda ya yaba da jarumtar jami’an tsaro
  • Gwamnan ya ba da tallafin fiye da N70m, ya kuma bayyana shirin daukar sababbin 'yan banga sama da 2,100 a fadin jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi magana kan harin ta'addanci da aka kai a Bauchi.

Gwamna Bala Mohammed ya tabbatar da cewa fiye da ‘yan bindiga 60 sun mutu a harin da aka kai kauyen Mansur a karamar hukumar Alkaleri.

Gwamna ya magantu kan harin yan bindiga
Bayan hallaka yan bindiga 60, gwamna ya ba da gudunmawa. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Asali: Facebook

Barnar da aka yi wa yan bindiga

Gwamnan ya fadi haka ne yayin ziyarar jaje da ya kai ranar Alhamis 15 ga watan Mayun 2025 a karamar hukumar Alkaleri, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin, wanda ya faru mako biyu da suka gabata, ya yi sanadiyyar mutuwar wasu ‘yan banga da kuma fararen hula daga kauyen.

Gwamna Bala ya ce mutane 21 sun mutu ciki har da yan banga 13 da fararen hula takwas.

Ya bayyana lamarin a matsayin babban kalubalen tsaro, amma ya ce jarumtar jami’an tsaro da yan sa-kai ya haddasa asarar ga ‘yan ta’addan.

Ya ce:

“Ko da sun jawo mana asara mai yawa, fiye da 60 daga cikinsu sun mutu. Don haka ba mu rasa mu kadai ba.
“Jami’an tsaro da matasanmu yan banga sun yi nasara duk da makaman da suka fi namu karfi."
Gwamna ya yi ta'aziyya bayan harin yan bindiga
Gwamna ya jajanta da yan bindiga suka kai hari a Bauchi. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Asali: Facebook

Harin yan bindiga: Gwamna ya yi ta'aziyya

Ya mika sakon ta’aziyya daga gwamnatin tarayya da na jihar, inda ya ce suna aiki da Ofishin Nuhu Ribadu don hana faruwar irin hakan.

“Mun zo da sunan gwamnati domin jajantawa, musamman ma mutanen Alkaleri, Gwana, Duguri, Yelwan Duguri da Bauchi.
“Ina mika sakon jaje na Gwamnatin Tarayya, musamman daga Ofishin Nuhu Ribadu. Za mu samu taimako sosai."

- A cewar Gwamna Bala

Ya sanar da tallafi na ₦5m ga kowace iyalan yan banga da aka kashe, ₦3m ga iyalan fararen hula, da ₦20m don ayyukan yan banga.

Haka kuma, ya bayyana shirin daukar yan banga fiye da 2,100 kafin shekara ta kare, inda za a fara da mutane 300 zuwa 500, Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya ce za a saka su cikin tsarin albashi, kuma za su samu horo daga jami’an tsaro domin hana tashin hankali.

Ya roki shugabannin gargajiya su taimaka wajen gano masu bayar da bayanai ga ‘yan bindiga domin kara inganta tsaro.

Gwamna Bala ya ce gwamnati na daukar matakai masu tsauri don kare rayukan al’umma daga barazanar ‘yan ta’adda.

'Yan bindiga sun hallaka mutane a Bauchi

Kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da mugayen makamai sun kai hari a ƙaramar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi.

Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a yayin harin da suka kai.

Ƴan bindigan sun kuma yi wa wasu ƴan sa-kai masu yin aikin sintiri kwanton ɓauna a cikin daji, wanda hakan ya jawo asarar rayuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.