Amarya da Ango da Wasu Mutane Sun Gamu da Jarabawa 'Mara Daɗi' a Jihar Katsina
- Ango da amarya da ba a daɗe da aurensu ba tare da wasu mutane da dama sun rasa gidajensu sakamakon guguwa da ruwa mai ƙarfi a Katsina
- Rahotanni sun nuna cewa mutane sun rasa gidaje da dukiyoyi na miliyoyin Naira daga abin da suka kira jarabawa daga Allah Madaukakin Sarki
- Sun roki gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhDta kawo masu ɗauki duba da ibtila'in da ya afka masu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Akalla gidaje 300 ne suka rushe, yayin da dukiyoyi na miliyoyin Naira suka salwanta, sakamakon wata guguwa mai haɗe da ruwan sama mai ƙarfi da aka yi a wasu unguwanni a jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba, jim kaɗan bayan sallar la’asar, inda aka ga rufin gidaje da katako na tashi sama suna shawagi a sararin samaniya.

Asali: Facebook
Channels tv ta rahoto cewa daga cikin wuraren da lamarin ya fi shafa akwai Sabuwar Unguwar Modoji Gabas, Shinkafi, Kukar-Gesa, da wasu yankuna na karamar hukumar Jibia.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ango da amarya sun rasa gidansu a Katsina
Mutane da dama, ciki har da wasu sababbin ma'aurata; ango da amarya da ba su daɗe da shiga daga ciki ba, sun rasa matsugunansu sakamakon iftila’in.
Wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa sun bayyana hakan a matsayin jarrabawa daga Allah.
Sai dai sun roƙi gwamnatin jihar Katsina da sauran masu hannu da shuni da su taimaka musu musamman duba da tsananin matsin tattalin arziki da ake ciki a ƙasar.
Wane hali mutane suka shiga bayan guguwar?
Ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Maryam Muhammad, ta ce:
"A lokacin da lamarin ya faru ina zaune a cikin ɗaki. Kwatsam ɗakina ɗaya tilo da nake da shi ya ruguzo kaina, har na ji rauni a kafa da hannuna."
"Na gode wa Allah yara na suna makarantar Islamiyya a lokacin. Muna roƙon taimakon Allah da kuma gwamnati saboda na sha wahala sosai har na siyar da duk dukiyata domin na gina wannan ɗaki guda ɗaya da ya rushe," in ji ta.

Asali: Facebook
Wani mutumi mai suna Mubarak Rabi’u, wanda shi ma lamarin ya shafa, ya bayyana irin wahalar da suke ciki, yana roƙon gwamnatin jihar ta kawo musu dauki.
"Mun amshi wannan kaddara da tawakkali, amma muna neman gwamnatinmu mai tausayi da ta dubi halin da muke ciki domin ta taimaka mana," in ji shi.
"A yanzu haka, ba mu san inda iyalanmu za su je ba, duba da halin talauci da muke fama da shi."
Wani magidanci da ake kira Malam Ado, wanda iska ta yaye kwanon gidansa ya shaidawa Legit Hausa cewa suna bukatar taimako daga gwamnati da masu hannu da shuni a halin da suke ciki.
Ya ce:
"Abin ba daɗi amma jarabawa ce daga Allah, mun karbe ta hannu biyu. Muna shirin yadda za mu tunkari daminaɓsai ga wannan lamarin.
"Muna kira ga gwamnati da sauran ƴan uwa su taimaka wa waɗanda wannan iska ta yi wa ɓarna, da yawa ba su da wani wurin zama sai nan din."
ACF ta bukaci a shiryawa ambaliyar 2025
A wani labarin, kun ji cewa manyan Arewa sun buƙaci gwamnatocim.jihohi da tarayya su ɗauki matakan kariya gabanin ambaliyar da ake hasashe a daminar bana.
ACF ta nuna damuwa kan hasashen da Hukumar Kula da Madatsun Ruwa ta Kasa (NIHSA) ta fitar, da ta ce akwai yiwuwar yin ambaliya a jihohi 30.
Kungiyar ta bukaci hukumomin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su kara himma wajen wayar da kai da shirye-shiryen kariya.
Asali: Legit.ng