'Talaka Ya Gaji,' Hakeem Baba Ahmad Ya ce Taliya ba za Ta Sayi Kuri'a a 2027 ba
- Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa duk tsalle-tsallen da ‘yan siyasa ke yi a yanzu ba shi da amfani saboda ba su da kishin jama'a
- Ya ce talakan Najeriya, musamman na Arewa, sun gaji da halin da ake ciki, kamar su matsalar abinci da tsaro da suka hana jama'a zaman lafiya
- Tsohon hadimin Kashim Shettima ya yi gargadin cewa idan ba a yi sauyi mai inganci ba, to talaka ne zai kwato hakkinsa a zabe mai zuwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mashawarcin Kashim Shettima, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce yawancin ‘yan siyasa da ke fafutuka da hada-kai a halin yanzu suna yin hakan ne kawai don biyan bukatunsu.
Ya ce a lissafin 'yan siyasa a yanzu, babu batun kwato hakkin talaka ko ciyar da rayuwar gaba, duk da halin da aka jefa shi a halin yanzu.

Asali: Facebook
Dr. Hakeem Baba Ahmad ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, wanda ya jawo ra'ayin jama'a da dama, musamman mabiyansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Halin yan siyasa daya ne,' Hakeem Baba Ahmad
A cewarsa, duk wani hadin gwiwa ko cakudewar ‘yan siyasa da ake gani yanzu ba zai kai ga wani sauyi ba, domin ‘yan siyasar duk iri daya ne da nufin su daya.
Ya ce:
“Duk tsalle-tsallen 'yan siyasan nan a banza ne. Sai sun gama taruwa a gefe daya, ko tattara wata shekar daga tsummokarar da suka lalata, sannan su bude ido su ga ashe duk kanwar ja ce."
'Talaka na son canji,' Dr. Hakeem Baba Ahmed
Ya jaddada cewa talaka, musamman a Arewacin Najeriya, ya gaji da yadda ake tafiyar da mulki. Yanzu haka, abin da yake nema ba rakiyar dan siyasa ba ce, sai dai tsaro da abinci.

Asali: UGC
Dr. Hakeem Baba Ahmad ya ce:
“Komin kudin ka, da taliyar ka da karfin ka a yanzu, ba dai kai zaka jefa kuri’a ba. Talakan da ka juya wa baya shi zai yi kuri’a. Ya kuma gaji."
Baba-Ahmed ya kara da cewa akwai yiwuwar talaka da aka raina ne zai farka ya karbi iko da kansa, musamman yayin babban zabe mai zuwa a 2027.
A kalamansa:
“Gefen (jam'iyya) da ke ramewa yana da aiki ja a gaban sa. Ko dai a yi sauyi mai zurfi da inganci ko kuma talaka ya nuna masu hanya. Talakan Arewa da aka raina, shi zai shiga gaba wajen kwatowa kansa ‘yanci.”
Hattara ‘yan zirga-zirga."
Hakeem Baba Ahmad ya shawarci su Kwankwaso
A wani labarin, mun wallafa cewa Dr. Hakeem Baba-Ahmed, tsohon mashawarcin Kashim Shettima, kan harkokin siyasa, ya shawarci Rabi'u Musa Kwankwaso da Peter Obi.
Baba-Ahmed ya bukaci Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP da Peter Obi na jam’iyyar LP da su hakura da sake tsayawa takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa, a ba matasa dama.
A cewar Baba-Ahmed, tsofaffin ‘yan takarar sun riga sun yi kokarinsu a baya, kuma babu wani sabon abu da za su kara kawo wa kasar, don haka lokaci ya yi da za su ba sababbin jini dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng