Da Gaske Peter Obi Ya Rushe Masallacin da 'Yan Arewa ke Sallah a Anambra? Gaskiya Ta Fito
- Shugabannin 'yan Arewa da ke zaune a jihar Anambra sun ce Peter Obi bai nuna musu wariya ba a lokacin da yake gwamna
- Sun karyata zargin cewa Mista Obi ne ya bayar da umarnin rushe wani masallaci a lokacin mulkinsa a Anambra
- 'Yan arewan sun ayyana cikakken goyon bayansu da tsohon gwamnan Anambra, Obi a zaben shugaban kasa na 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra, Nigeria - Shugabannin 'yan Arewa mazauna Anambra sun yi watsi da zarge-zargen cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya nuna wariya ga ‘yan Arewa a lokacin da yake gwamna.
Shugabannin, wadanda suka yi magana a wasu hirarraki daban-daban da manema labarai a Onitsha da Awka, sun kuma karyata ikirarin da wasu abokan hamayyar siyasar Obi ke yi cewa ya rushe wani masallaci a lokacin mulkinsa.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa

Source: Facebook
Sun bayyana zarge-zargen a matsayin kalaman siyasa da aka kirkira domin bata sunan Obi gabanin babban zaben 2027, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Peter Obi ya tallafa wa yan Arewa
A cewar shugabannin, ‘yan Arewa da ke Anambra sun kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin Obi, inda suka amfana da wasu shirye-shiryen gwamnatinsa.
Sun ce daga cikin abubuwan da suka amfana da su akwai ilimi kyauta, rancen noma da kuma daukar nauyin wasu ‘yan Arewa zuwa aikin Hajji na shekara-shekara.
Daga cikin wadanda suka yi magana akwai sakataren kungiyar yan Arewa Arewa mai kula da jihohin Anambra da Delta, Mahmud Ibrahim; Sarkin Hausawan Awka, Alhaji Garba Haruna; da shugaban al’ummar Arewa a Anambra, Alhaji Gidado Sidikki.
Da gaske Peter Obi ya rushe masallaci?
Ibrahim, wanda ya ce ya shafe shekaru da dama yana rike da mukamin sakataren al’ummar Arewa, ya ce zargin Obi da rushe masallacin ba gaskiya ba ne.
Ibrahim ya ce masallacin da ake magana a kai an rushe shi ne kafin Obi ya zama gwamnan jihar Anambra.
Ya bayyana cewa masallacin ya rushe ne a watan Fabrairun 2006 yayin wani rikici da ya biyo bayan rikicin Shari’a, yayin da Obi ya zama gwamna a watan Maris na wannan shekarar.

Source: Facebook
Ibrahim ya kuma karyata zargin cewa Obi ya tilasta wa ‘yan Arewa karbar katin shaida domin su ci gaba da zama a Anambra.
Ya ce katunan shaidar da al’ummar Arewa suka raba wani shiri ne na al’ummar domin tantance ‘yan uwansu, yayin da katin ANIDS ya shafi dukkan mazauna jihar.
Sarkin Hausawa ya kare Obi
Sarkin Hausawan Awka, Alhaji Garba Haruna, ya ce bai taba ganin wata manufa daga gwamnatin Obi da ta nuna bambanci tsakanin ‘yan asalin jihar da wadanda ba ‘yan asalin jihar ba ba.
Ya ce ‘ya’yansa sun amfana da shirin ilimi kyauta na Obi, yayin da shi kansa ya amfana da tallafin da gwamnatin ta bayar domin aikin Hajji.
Sun bayyana cewa zarge-zargen na da nasaba da siyasa, inda suka ce za su hada kan ‘yan Arewa mazauna Anambra domin mara wa Obi baya yayin da yakin neman zaben 2027 ya fara.
Peter Obi ya tada mahawa a sohiyal midiya
A baya, kun ji cewa Peter Obi ya ce ya ziyarci dukkan makarantun sakandare na jiharbAnambra lokacin da yake gwamna, lamarin da ya jawo muhawara aNkafafen sada zumunta.
Obi ya ce ya dace shugabannin siyasa su rika ba bangaren ilimi muhimmanci ta hanyar kai ziyara akai-akai zuwa makarantun firamare, sakandare da jami'o'i
Asali: Legit.ng

