Hisbah Ta Kai Samame a Yobe, Ta Rufe Otal bayan Ta Ƙwace Kwalayen Giya

Hisbah Ta Kai Samame a Yobe, Ta Rufe Otal bayan Ta Ƙwace Kwalayen Giya

  • Hukumar Hisbah ta Yobe tare da NDLEA da NSCDC sun rufe 'Maina Lodge' a Damaturu, inda suka kama katon 209 na giya
  • Shugaban hukumar, Dr. Yahuza Abubakar, ya ce an gano giya a motar 'Golf' da kuma daki na musamman a otal din da aka bincika
  • Ya ce gidan haya da ake zargin ana amfani da shi wajen fasikanci shi ma an rufe, yayin da bincike ke ci gaba a jihar Yobe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta rufe otal din Maina Lodge a Damaturu.

Hukumar Hisbah tare da hadin guiwar hukumomin NDLEA da NSCDC sun yi nasarar kama katon 209 na giya a birnin da ke jihar Yobe.

Hisbah ta rufe otal bayan kwace giya
Hisbah ta kwace katon din giya a Yobe. Legit.
Asali: Original

An rufe otal a Yobe bayan kama giya

Shugaban hukumar, Dr. Yahuza Hamza Abubakar, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai da ya yada bidiyon a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubakar ya ce sun kai samame kan wata mota kirar Golf mai lamba ABJ-144-SC da aka loda giya a cikin 'Maina Lodge'.

Ya ce an gano karin kwalabe 34 na giya a dakin manyan baki na 07 na otal din, bayan an ci gaba da bincike a wajen.

Abubakar ya kara da cewa, an rufe otal din na dan lokaci har sai an kammala bincike don gano direban da masu shigowa da kayan haram.

Ya ce:

“Zan gaya muku cewa muna aiki da masu otal din don gano wadanda ke da hannu cikin wannan aika-aikar."

A wani lamari daban, shugaban ya ce hukumar ta dauki mataki bayan wani korafi daga wani Waziri Ibrahim dangane da gidan da ake zargin fasikanci.

Ya ce an rufe gidan na haya na tsawon watanni uku domin ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Hisbah ta rufe otal a Yobe
Hukumar Hisbah ta rufe otal bayan kama giya da dama. Hoto: NDLEA.
Asali: Facebook

Hisbah ta yabawa Gwamna Mai Mala Buni

Shugaban ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe bisa goyon bayansa gare su tare da jinjinawa jami’an tsaro bisa hadin kai da suke bayarwa.

Ya kara da cewa:

“Wadannan nasarori na nuna irin jajircewarmu wajen kare tarbiyya da yaki da miyagun dabi’u a jihar Yobe."

Abubakar ya sake jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da aiwatar da dokokin da suka haramta giya da ayyukan fasikanci a jihar.

Ya bukaci jama’a su rika kai rahoton duk wani abin da ya saba doka, ya ce bincike na ci gaba da gudana domin tabbatar gano bakin zaren.

Kano: Hisbah ta kama dubban kwalaben giya

Kun ji cewa Hukumar Hisbah a jihar Kano ta yi nasarar cafke wata mota makare da kwalaben giya akalla 8,600 tare da direban motan.

An kama motar ne a kusa da kauyen Kwanan Dangora bayan da 'yan Hisbah sun yi ta bibiyar motar tun daga jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

'Yan Hisban sun kuma kama wasu 'yan mata akalla 15 a wurare daban-daban a jihar ta Kano da ake zargi da yin karuwanci cikinsu har da wadanda aka kama a baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.