Mutuwa Ta Sake Girgiza Najeriya, Tsohon Antoni Janar Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Mutuwa Ta Sake Girgiza Najeriya, Tsohon Antoni Janar Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Tsohon Antoni-Janar kuma kwamishinan shari'a na Jihar Legas, Farfesa Alfred Kasunmu, ya riga mu gidan gaskiya
  • Kasunmu ya kasance Babban Lauyan Najeriya (SAN) kuma tsohon shugaban tsangsyar koyar da harkokin doks na Jami’ar Legas
  • Marigayin ya kuma yi aiki a matsayin Antoni-Janar na jihar Legas daga daga shekarar 1975 zuwa 1978

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Tsohon Antoni-Janar na Jihar Legas, Farfesa Alfred Kasunmu, ya rasu a safiyar Lahadi, 9 ga Agusta, 2026.

Kasunmu, wanda yake Babban Lauyan Najeriya (SAN), ya rasu cikin kwanciyar hankali, kamar yadda iyalansa suka bayyana a wata sanarwa.

Alfred Kasunmu.
Tsohon Antoji Janar na jihar Legas kuma babban lauya a Najeriya, Farfess Alfred Kasunmu Hoto: @the_dailygist
Source: Twitter

The Cable ta rahoto cewa iyaalansa sun bayyana marigayin a matsayin fitaccen malami, mai ba da shawara da kuma uban iyali, wanda ya bar tarihi mai cike da hikima, mutunci da hidima da suka zama abin koyi ga al’ummomi masu zuwa.

Kara karanta wannan

Bayan haduwa da Tinubu, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya gana da Wike

Sanarwar ta ce:

“Farfesa Kasunmu ba uban iyalinmu ne da muke matukar kauna kawai ba, ya kasance fitaccen malami, mai ba da shawara kuma Babban Lauya a Najeriya."

Ya sadaukar da rayuwarsa ga shari’a

Iyalin sun ce Kasunmu ya taimaki rayuwar mutane da dama ta hanyar sadaukar da kansa ga fannin shari’a, ilimi da kuma jin kai.

Sun bayyana cewa za a sanar da cikakken tsarin jana’izar daga baya, yayin da aka shirya zaman makoki a gidansa ranar Asabar, 15 ga Agusta, da Lahadi, 16 ga Agusta, daga karfe 1:00 na rana zuwa 7:00 na yamma.

Iyalin sun kuma bukaci jama’a da su yi addu’a a lokacin makokin, suna mai cewa suna samun kwanciyar hankali ne daga tunawa da irin rayuwar da marigayin ya yi.

Kasunmu ya fara aikin lauya a 1964

Marigayi Kasunmu ya zama cikakken lauya a Najeriya a 1964, sannan a wannan shekarar ya shiga Faculty of Law ta Jami’ar Ife, wadda yanzu ake kira Jami'sr Obafemi Awolowo, a matsayin daya daga cikin malaman farko na jami’ar.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya shiga damuwa bayan tura kudi masu yawa a asusunsa

A shekarar 1971, ya koma Jami’ar Legas inda ya zama babban malami. Shekaru biyu bayan haka, a 1973, aka nada shi Farfesa a fannin shari’a, sannan ya rike mukamin shugaban tsangsya daga 1973 zuwa 1975.

Lagos.
Taswirar jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya zama Antoni-Janar na Legas

Marigayi Kasunmu ya yi aiki a matsayin Antoni-Janar na Jihar Legas daga shekarar 1975 zuwa 1978, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Bayan ya kammala wannan aiki, ya koma aikin lauya mai zaman kansa, inda ya kafa kamfanin lauyoyi na Prof. A.B. Kasunmu Chambers. Baya ga aikin lauya da koyarwa, Kasunmu ya kasance fitaccen marubucin littattafan shari’a.

Tsohon daraktan Majalisar tarayya ya rasu

Kun ji cewa tsohon Darakta Janar kuma Magatakardan Majalisar Tarayya na farko, Dr. Adamu Mohammed Fika, ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin, wanda ke rike da sarautar Zarma Kura na Fika, ya riga mu gidan gaskiya ne a wani asibiti da ke babban birnin tarayyya, Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan uwa, abokan aiki da sauran masu alaka da marigayi Dr. Muhammad Fila sun fara bayyana alhininsu kan rasuwarsa tare da mika sakon ta'aziyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262