Arewa
Kimanin rayukan mutane 7 ne suka salwanta yayin da wani mummunan hatsarin mota ya auku a a kan wata babbar hanya a kauyen Kwalande dake karamar hukumar Maigatari a jihar Jigawa dake Arewa maso Yammacin Najeriya.
'Yan daban daji kimanin 17 sun afka tarkon rundunar dakarun sojin kasa ta Najeriya, yayin da rayuwar daya daga cikin 'yan ta'addan ta salwanta biyo bayan wani simame na sharar daji da dakaru suka kai a jihar Katsina.
Wata kungiyar jam'iyya mai mulki ta APC wadda ake yiwa lakabi da G8, a ranar lahadi ta bayyana goyon baya a kan irin kokarin da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ke yi wajen tafiyar da al'amuran gwamnatin jihar a yanzu.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ba gwamnatinsa bane ta gina bangaren gadar Abubakar Audu da ke hanyar BUK daura da Gadon Kaya ta da fara tsagewa. Martanin da tsohon gwamnan ya yi a ranar Juma'a na da
A ranar 17 ga watan Yulin 2019, gwamnatin kasar Amurka ta gabatar da kyautar shekara ga wadanda suka nuna karfin hali da mafi kololuwar gwarzantaka wajen karrama dan Adam ba tare da nuna wariyar akidar addini ba.
Karshen tika-tik kuma komai nisan dare gari zai waye domin kuwa a yau Talata, 23 ga watan Yulin 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da sunayen ministocin sabuwar gwamnatin sa a zauren majalisar dattawa.
Da yake dai a koda yaushe na gari ba sa karewa duk da dai a wannan zamani sai an tona, mun samu cewa wani karamin ma'aikacin sojan sama na Najeriya, Bashir Umar, ya yi tsintuwar dukiya mai tarin yawa kuma ya mayar wa da mai ita.
Cikin karsashi na bayyana farin ciki, gwamnan jihar Kastina Aminu Bello Masari, ya yi karin haske da cewar ba tare da daukar wani lokaci mai tsawo ba rashin tsaro da ta'addancin 'yan daban daji zai zamto tarihi a jihar.
A yayin da ake tantance arzikin kowace kasa da girman tattalin arzikin ta da kuma adadin al'ummar da ta kunsa gami da harkokin kasuwanci, mun kawo muku jerin wasu jihohin Najeriya 20 mafi arziki a bana.
Arewa
Samu kari