Sufeton Ƴan Sanda Ya Ja Kunne kan Zargin an Boye Masu Laifi a Gidan Gwamnatin Osun

Sufeton Ƴan Sanda Ya Ja Kunne kan Zargin an Boye Masu Laifi a Gidan Gwamnatin Osun

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ana zargin wasu jam'iyyun siyasa a Osun na boye wasu mutanen da ake zargi da aikata laifuffuka
  • Sufeto Janar na 'yan sanda, Olatunji Disu, ya ce an kuma ba shi rahoton cewa ana boye wasu da ake nema a Gidan Gwamnatin jihar Osun
  • Tuni Gwamna Ademola Adeleke ya bukaci a kama duk wanda ya aikata laifi, ko da ɗansa ne, tare da neman cikakken bincike kan tashin hankali a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun – Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya bayyana cewa bayanan sirri da aka gabatar masa sun nuna cewa wasu jam'iyyun siyasa a jihar Osun na 'boye mutanen da ake zargi da aikata laifuffuka.

Kara karanta wannan

"Ni ba ungulu ba ne:" Ganduje ya yi martani ga zargin zai hade da Kwankwaso

Olatunji Disu ya bayyana haka ne a Osogbo, babban birnin jihar Osun, yayin wata ziyarar da ya kai wa Gwamna Ademola Adeleke.

Tunji Disu ya yi magana kan boye masu laifi a gidan gwamnati
Sufeton yan sandan Najeriya Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta wallafa cewa Sufeton yan sanda ya kuma ce Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Ibrahim Gotan, ya sanar da shi cewa akwai wasu mutane da jami'an tsaro ke nema da ake zargin suna cikin Gidan Gwamnatin jihar.

Yan sanda sun zargi jami'an gwamnati

Jaridar Daiily Post ta wallafa cewa Kwamishinan 'yan sandan ya sanar da shi cewa ana zargin an boye mutanen a gidan gwamanti duk da sun aikata laifi.

Ya ce:

"Idan na ce ban samu koke-koke ba, zan yi ƙarya. Kwamishinan 'yan sanda ya shaida min cewa akwai wasu mutane da yake nema da suke cikin Gidan Gwamnati. Na tambaya, idan hakan gaskiya ne, me ya sa ake barin wadanda ake zargi a Gidan Gwamnati? Amma na gaya masa cewa a matsayinsa na jami'in da ke kula da tsaro, ya san yadda zai bi wajen magance lamarin. Na kuma ji cewa wannan jam'iyya da waccan jam'iyya suna boye da wadanda ake zargi da aikata laifuka."

Kara karanta wannan

Zargin badakalar Gbajabiamila: Jam'iyyar NDC ta mika bukata ga Tinubu da EFCC

Olatunji Disu ya tabbatar da cewa rundunar 'yan sanda za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar, tare da neman hadin kai wajen saukaka ayyukanta.

Gwamna zai ba yan sanda hadin kai

Da yake mayar da martani, Gwamna Ademola Adeleke ya bukaci rundunar 'yan sanda ta kama duk wanda aka samu da hannu a aikata laifi ba tare da la'akari da matsayinsa ba.

Ademola Adeleke ya yi alkawarin ba yan sanda hadin kai
Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke a gaban wani taro Hoto: Ademola Adeleke
Source: Twitter

Ya ce:

"Idan ka ga wani daga cikin mutanena ya aikata laifi, ku kama shi. Idan ma ɗana ne ya aikata laifi, ku kama shi domin ya koyi darasi. Wannan shi ne abin da nake fada a gaban Sufeto Janar."

Gwamnan ya kuma yi gargadin kada a bari rashin doka ya mamaye jihar, tare da neman a gudanar da bincike kan kashe-kashe da sauran laifuffukan tashin hankali da suka faru.

Yan daba sun yi barna a Osun

A wani labarin, kun ji cewa wasu mahara da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun harbi wani ’dan jam'iyyar APC, Taofeek Mustapha a jihar Osun yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a jhar.

Kara karanta wannan

Sheikh Mansur Sokoto: Ma'anar batanci ga Annabi Muhammad SAW da hukuncinsa a Musulunci

Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da samun rigingimun siyasa gabanin zaben gwamnam jihar Osun da za a yi a watan Agusta, 2026 duk da tsawatarwa da jami'an tsaro ke yi na a yi siyasa a cikin lumana.

Jigon APC da aka harba da bindiga, Taofeek Mustapha ya ce yana sanye da hular kamfen mai tambarin AMBO lokacin da aka kawo hari, kuma sai da aka tabbatar yana sanye da hular tallan AOC kafin a harbe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng