Musa Mai Sana'a Ya Magantu kan Jita Jitar Rashin Lafiya da Mutuwarsa da Ake Yaɗawa
- Fitaccen jarumin Kannywood, Musa Mai Sana'a, ya yi magana bayan yaɗuwar jita-jitar rashin lafiyarsa da mutuwarsa, inda ya fayyace gaskiyar abin da ya faru
- Jarumin ya bayyana cewa yana cikin ƙoshin lafiya, ya ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa tare da yin addu'ar Allah ya shiryar da masu yaɗa ƙaryar
- Mai Sana'a ya kuma bayyana matsayarsa kan tafiyar Triple R Kannywood, yana mai tabbatar da cewa har yanzu yana goyon bayan Shugaba Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Bayan yada jita-jitar rashin lafiyarsa da mutuwa, ɗan wasan Kannywood ya yi karin haske kan lamarin.
Fitaccen ɗan wasan kwaikwayo a Kannywood, Musa Mai Sana'a ya bayyana halin da yake ciki game da raɗe-raɗin da ake yaɗawa.

Source: Facebook
Jarumin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ake hira da shi wanda DCL Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan
Mutumin da ya sayar da yaron abokinsa a kan N1.3m ya tona yadda suke satar yara a Najeriya
Mai Sana'a ya karyata batun rashin lafiya, mutuwarsa
Musa Mai Sana'a ya ƙaryata abin da ake yaɗawa inda ya ce kwata-kwata bai kwanta rashin lafiya ba.
Ya yi addu'ar Allah ya shirya masu yada karyar inda ya ce babu wanda ya fi ƙarfin shiga jarabawa a rayuwarsa.
Ya ce:
"Ana ta kiraye-kiraye a waya wai ban da lafiya ko kuma na mutu, ni ma wayar gari na yi na samu wannan ƙalubalen.
"Ni dai na san ban kwanta wata rashin lafiyar komai ba, idan na kwanta kai ma (dan jarida) za ka sani.
"Lafiya ta kalau, idan ina da wata lalura za ka sani, amma ban san gobe ba saboda Allah ne ke da ikon haka."

Source: Facebook
Mai Sana'a ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu
Game da tafiyar Triple R Kannywood wanda ke goyon bayan Bola Tinubu, Mai Sana'a ya fadi matsayarsa a kungiyar.
Ya ce har yanzu yana kan akidar goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da kuma kasancewa cikin kungiyar.
Har ila yau, ya yabawa gwamnatin Bola Tinubu inda ya ce ba shi da dan takara kamar shi haka jam'iyyar APC yake yi tun tuni.
"Har yanzu ina kan akida ta, ta Bola Ahmed Tinubu, saboda ina sonshi a siyasance kuma na ga zan iya yin tafiyar babu wanda ya saka ni."
- Musa Mai Sana'a
Musa Mai Sana'a ya tabbatar da cewa yana cikin tafiyar Triple R Kannywood wanda Dauda Kahutu Rarara ke jagoranta duk da matsalolin da ake samu da ya jawo ficewar wasu a kungiyar.
Tinubu: Rikadawa ya balle daga tafiyar Rarara
A wani labarin, kun ji cewa fitaccen jarumin Kannywood, Rabiu Rikadawa, ya sanar da ficewarsa daga ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope.
Rikadawa ya bayyana matakin ne a ranar Juma'a, 3 ga watan Yulin 2026, yana tabbatar da cewa ya fice daga tafiyar.
Jarumin ya ce ya fice daga ƙungiyar da mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ke jagoranta, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.
Asali: Legit.ng
