Sallah Babba: Kasuwar raguna ta yi kasa a jihar Kebbi
A dai-dai lokacin da ya rage kasa da kwanaki bakwai a gudanar da bukukuwan babbar sallah, a jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, raguna na nan jibge a kasuwanni masu saya sun yi karanci.
A wannan shekarar, da dama daga cikin masu sayen ragunan layya da wuri-wuri kamar yadda aka saba a baya, ba su halarci kasuwanni ba har ya zuwa yanzu.
Masu sayar da dabbobi a jihar Kebbi sun koka da yadda kasuwarsu ta yi kasa a bana sabanin yadda ta kasance a bara. Sai dai sun alakanta rashin samun ciniki da rashin kudade a hannun mutane.
Shugaban kungiyar masu sayar da raguna a Birnin Kebbi, Alhaji Ibrahim Mairago, ya ce rashin wadatattun kudade a hannun mutane ya sanya kasuwar raguna ta yi kasa duk da 'yan kasuwa sun jibge dabbobinsu ga mabuka masu saye.
Wasu daga cikin masu niyyar sayen raguna a bana, sun bayyana fahimtarsu kan yadda kasuwar dabbobin ke kasancewa a bana. Da yawa sun koka da yadda ragunan layya suka yi tsada a bana wadda ta kere ta bara.
KARANTA KUMA: Afuwa: Gwamnan Zamfara ya sallami fulanin daji 100 daga dauri
A yayin da masu niyyar sayen ragunan layya ke koka wa da tsadar a bana, Alhaji Mairago ya ce akwai yiwuwar farashin dabbobi zai yi tashin doron zabuwa a yayin da gwamnatin jihar Kebbi ke gab da biyan ma'aikata albashin su na wata.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng