Emefiele: Shekara 1 da Rasuwa An Nemi a Jefa Marigayi Buhari a Shari'ar Satar $6.2m
- Jim Obazee ya yi magana a kotu a matsayin shaida a shari’ar da EFCC ta ke yi da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- Mai binciken na musamman da gwamnatin Bola Tinubu ta dauka haya ya bukaci hukuma ta yi shari’a da Muhammadu Buhari
- Ban da tsohon shugaban kasar, Obazey ana so a hada da Boss Mustapha da wasu jami’an bankin CBN a shari’ar satar $6m
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Wani mai bincike na musamman da Bola Ahmed Tinubu ya dauka haya, Jim Obazee, ya bada shawarar kai Muhammadu Buhari kotu.
Jim Obazee yana so a binciki rawar da ake zargin marigayi Muhammadu Buhari da Boss Mustapha sun taka wajen cire $6.2m daga bankin CBN.

Source: Getty Images
Obazee yana so a kai Muhammad Buhari kotu
The Nation ta ce Obazee ya yi wannan magana ne a ranar Juma’a da yake ba da shaida a shari’ar da ake yi tsakanin Godwin Emefiele da EFCC.
Hukumar EFCC sun yi karar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya na CBN a kotun tarayya, ana tuhumarsa da aikata wasu laifuffuka 20 a ofis.
Mista Obazee ya ce a sakamakon kin daukar mataki ko kuma wasu matakan da ya dauka, ya kamata ya zama har marigayi Buhari ake tuhuma a kotu.
Shari'a a kotu da mutumin da ya rasu?
Ba tsohon shugaban kasar ba, Obazee yana so shari’ar ta shafi Boss Mustapha wanda shi ne Sakataren gwamnatin tarayya lokacin na Buhari.
Ya ce:
"Ya kamata a yi karar Buhari tare da Godwin Emefiele a shari’ar nan ta satar $6.2m, ko da bayan ya rasu ne, tunda ana bada lambar yabo bayan mutuwa.
A game da Boss Mustapha, a iyaka sani na, ya karyata cewa ya sa hannu a takardun da suka bukaci a taba $6.2m har suka jawo aka cire wannan kudi zuwa ga wani da yake ikirarin ma’aikaci ne a ofishinsa.
Duk abin da ake yi wa Emefiele na binciki, ya kamata a yi wa Buhari, Boss, Miashanu da tsofaffin shugabannin CBN a karkashin Emefiele.

Source: Getty Images
Ana so a hada da ma'aikatan CBN a kotu
Jaridar The Cable ta ce mai binciken yana son ganin Bashirudeen Maishanu a kotu, wanda ya yi ikirarin ya dawo masa da kudi har $856,500.
Shi Bashirudeen Maishanu ma’aikacin CBN ne da ake zargin ya dauki kudin kuma ya dawo wa kwamitin bincike da wadannan makudan daloli.
Lauyan masu kara, Rotimi Oyedepo (SAN) ne ya kira Obaze a kotu, shi kuma a nan ya duba takardun kotu, ya ce za a iya wanke Boss Mustapha ba.
Shi yana ganin har manajan bankin CBN da ke Abuja yana da laifi da aka fitar da kudi ba da saninsa ba, haka zalika ya bukaci a kama Jibril Abubakar.
Lauyan wadanda ake kara, Matthew Burkaa (SAN) ma ya yi wa Obaze tambayoyi har ya tabbatar da bai samu kudi hannun Godwin Emefiele ba.
A karshen zaman da aka yi, Alkali Hamza Mu'azu ya daga shari’ar sai 20 ga watan Oktoba 2026.
An sa hannun Buhari an saci kudi a CBN
Labarin nan ya yi bayanin yadda wani shaidan EFCC ya ce an yi amfani da sa hannun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na bogi domin yin sata.
Dala miliyan 6.23 aka sace daga CBN a lokacin gwamnatin tsohon gwamnan , Godwin Emefiele, da ake zargin an yi amfani da su da sunan aikin zaɓen 2023.
An samo takardun da suka bayar da izinin fitar da kuɗin, aka kuma yi tambayoyi ga waɗanda ke da hannu, yayin da Emefiele ke fuskantar tuhume-tuhume 20 a kotu.
Asali: Legit.ng


