Kano: 'Yan Tijjaniyya Sun Ajiye Dan Takarar Kwankwaso a Gefe, Sun Bi Abba
- Rahotanni sun nuna cewa majalisar shura ta Ɗariƙar Tijjaniyya ta ayyana goyon bayanta ga tazarcen gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a zaben 2027
- A wani taron da ta yi, majalisar ta ce ta yanke matayar ne saboda abin da ta bayyana a matsayin nagartaccen shugabancin da Abba Kabir ya nuna
- A na shi bangaren, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa shugabannin majalisar bisa addu'o'i da goyon bayan da suke cigaba da ba si a jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rahotanni sun nuna cewa Gwammna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar APC ya samu gagarumin goyon bayan 'yan Darikar Tijjaniyya.
Gwamnan ya samu goyon bayan 'yan Darikar ne a daidai lokacin da aka tsayar da tsohon mataimakin shi, Aminu Gwarzo takarar gwamna a NDC.

Kara karanta wannan
2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya wallafa labarin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Tijjaniyya ta goyi bayan Abba
Shugaban Majalisar Shura ta Ɗariƙar Tijjaniyya, Sheikh Sani Shehu Maihula, ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga tazarcen Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Sheikh Sani Shehu Maihula ya bayyana wannan matsaya ne yayin taron Zikiri da addu'ar ƙasa na shekara-shekara da Ɗariƙar Tijjaniyya ta shirya a fadar mai martaba sarkin Kano.
An bayyana cewa ɗan'uwansa kuma kakakin majalisar, Sheikh Ibrahim Shehu Maihula (Shehi Shehi), ya gabatar da jawabin maraba a madadinsa.
Dalilin neman tazarcen Abba
A cewarsa shehin, mambobin majalisar shura ta Ɗariƙar Tijjaniyya sun cimma matsaya guda cewa za su mara wa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya domin ya sake tsayawa takara karo na biyu saboda jajircewarsa.
Sanarwar ta kara da cewa sun ce ya dage wajen gudanar da shugabanci nagari, bunƙasa martabar addinin Musulunci da kuma aiwatar da manufofin da ke amfanar al'umma.

Kara karanta wannan
Hadimin Abba ya nanata zargin da ake yi wa Abdusalam Gwarzo na yin kwana da N308m
Malamin ya yaba wa gwamnan kan ci gaba da tallafa wa harkokin addini, ilimi, lafiya, bunƙasa abubuwan more rayuwa da shirye-shiryen jin daɗin al'umma a faɗin jihar Kano.
Martanin Abba Kabir Yusuf
Da yake mayar da martani, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna godiyarsa ga shugabanni da mambobin majalisar shura ta Ɗariƙar Tijjaniyya bisa addu'o'i, amincewa da kuma goyon bayan da suka nuna masa.
Ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da yi wa al'ummar Kano hidima cikin gaskiya, adalci da tsoron Allah, tare da alƙawarin ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar jama'a.

Source: Facebook
Haka kuma ya gode wa shugabannin addini a jihar bisa addu'o'insu da shawarwarinsu, yana mai cewa su abokan hulɗa ne masu muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Kano.
Tijjaniyya ta yi korafi a jami'o'i
A wani labarin, kun ji cewa jagoran Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya yi magana kan ba su masallatai a jami'o'i.
Ya bayyana cewa lokacin da za su cigaba da yin shiru ya kare, inda ya yi barazanar zuwa kotu idan ba a biya masu bukatarsu ba.
Jagoran Darikar ya ce ba su yarda duk wanda ba ya cikin akidar su ya jagorance su ba, inda ya bukaci a ba su fili ko a mika masu masallaci.
Asali: Legit.ng