Manoman Tumatir a Kano na asarar kaso 40% na amfanin gona a duk shekara

Manoman Tumatir a Kano na asarar kaso 40% na amfanin gona a duk shekara

Kamar yadda wani kwararre a kan tsimi da tanadin amfanin gona ya bayyana, manoman tumatir a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, na tafka babbar asara ta kimanin kaso 40 cikin 100 na amfanin gona a duk shekara.

Injiya Umar Mukhtar, kwararre a kan tanadi da sarrafa amfanin gona da kayan abinci, shi ne ya bayar da shaidar hakan a ranar Laraba yayin horas da manoman tumatir yadda ake tanadi da kuma sarrafa amfanin gona.

Jaridar Kano Today ta ruwaito cewa, babban bankin duniya tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi na sarrafa kayan abinci, da kuma masu bin diddigi wajen bunkasa jin dadin rayuwar al'umma, su ne suka daukin nauyin horas da manoman tumatir a jihar Kano.

Mista Mukhtar ya bayyana cewa, rashin kayayyaki da kuma injina na fasahar zamani masu sarrafawa da kuma tanadin amfanin gona, ya sanya manoman tumatir ke asarar amfanin gonakinsu a duk shekara.

KARANTA KUMA: Rage cin nama zai taimaka wajen magance sauyin yanayi - UN

A yayin tabbatar da sananniyar al'adar nan ta "Kanon Dabo tumbin giwa, ko da me kazo an fika", kwararren injiyan ya ce jihar Kano ta kasance a kan gaba wajen samarwa da kuma noman tumatir a duk ilahirin Arewacin Najeriya.

Sai dai ya bayyana takaicinsa dangane da yadda binciken da babban bankin duniya ya gudanar ya tabbatar da cewa manoman tumatir na tafka asarar kaso 40 cikin 100 na amfanin gonarsu a duk shekara.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel