An Shiga Jimami: Tsohon Sakataren Gwamnati da 'Yan Bindiga Suka Harba Ya Mutu
- Farfesa David Salifu, tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Benue, ya rasu sakamakon harbin da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka yi masa
- Rahotanni sun ce maharan sun tare motarsa a kan hanyar Wukari zuwa Zakibiam, inda suka bukaci ya hau babur kafin daga bisani suka harbe shi
- Salifu ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benue da ke Makurdi, bayan an kai shi can domin samun kulawar gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Benue – Tsohon sakataren gwamnatin jihar Benue (SSG), Farfesa David Salifu, ya rasu bayan harbin bindiga da ya samu a wani hari da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon sakataren gwamnatin ya rasu ne da sanyin safiyar Juma’a yayin da yake karbar magani a asibiti.

Source: Facebook
Tsohon sakataren Benue ya mutu
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun farmaki Farfesa Salifu a ranar Alhamis a kan hanyar Wukari zuwa Zakibiam da ke kan iyakar jihohin Benue da Taraba.
An ce Farfesa Salifu, wanda ya taba zama SSG a gwamnatin tsohon gwamna Gabriel Suswam, yana tafiya ne daga Wukari a jihar Taraba zuwa Makurdi a Benue lokacin da maharan suka tare motarsa a wajen garin Wukari.
Shaidu sun ce maharan, wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun umarce shi da ya sauko daga mota ya hau babur, amma daga bisani suka harbe shi bayan ya nuna masu turjiya.
Marigayin ya kasance malami ne a Jami’ar Tarayya da ke Wukari, kamar yadda rahoton ya nuna
Abokin marigayin ya tabbatar da rasuwar
'Dan takarar Sanata na ADC a Benue ta Kudu kuma aminin marigayin, Chief David Olofu, ya tabbatar da rasuwar a wata hira ta waya da manema labarai.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa masu koyon karatun Alkur'ani wuta a Bauchi
“Ya kasance mamba a kwamitin yakin neman zabena kuma amini ne na kud da kud. Na samu labarin cewa yana kan hanyarsa daga Wukari zuwa Benue lokacin da wasu bata-gari suka tare shi suka harbe shi,” in ji Olofu.
Ya kara da cewa an fara kai shi asibitin koyarwa da ke Wukari, kafin daga baya jami’ar ta samar da motar daukar marasa lafiya da likitoci domin kai shi samun karin kulawa.
Daga bisani aka kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benue da ke Makurdi, inda ya rasu da sanyin safiyar Juma’a.

Source: Original
Ana ta aika sakonnin ta’aziyya
Rasuwar Farfesa Salifu ta jawo dimbin sakonnin ta’aziyya a shafukan sada zumunta, kamar yadda Legit Hausa ta gani.
Dan takarar Sanata na Benue ta Kudu, Fasto Dave Ogbole, a shafinsa na Facebook, ya bayyana marigayin a matsayin mutum nagari wanda ya taba rayuwar mutane da dama da hikima da tausayi.
Fasto Ogbole ya ce mutuwar Salifu abin takaici ne da ke nuna yadda matsalar tsaro ke ci gaba da barazana ga rayukan al’umma a Najeriya.
'Yan bindiga sun sace fasto a Benue
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun sake yin aika-aika a jihar Benue bayan da suka yi garkuwa da wani fasto da ke jagorantar wani coci.
Hatsabiban 'yan bindigan sun sace faston ne tare da wasu mambobin cocinsa bayan sun kai harin da ya sake jefa mutane cikin firgici.
An mika kokon bara ga jama'a da su yi addu'o'i domin ganin mutanen da aka sace sun kubuta daga hannun 'yan bindiga cikin koshin lafiya.
Asali: Legit.ng

