Abubuwa 8 da baku sani ba game da Imam Abdullahi

Abubuwa 8 da baku sani ba game da Imam Abdullahi

A ranar 17 ga watan Yulin 2019, gwamnatin kasar Amurka ta gabatar da kyautar shekara ga wadanda suka nuna karfin hali da mafi kololuwar gwarzantaka wajen karrama dan Adam ba tare da nuna wariyar akidar addini ba.

Daya daga cikin mutane biyar da suka samu wannan karamci ya kasance wani Limami a Najeriya, Imam Abubakar Abdulla, wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen kubutar daga kiristoci 262 daga halaka a hannun 'yan daban daji.

Manyan malaman addini da suka samu kyautar kasar Amurka a taron ta da gudanar mai taken 2019 International Religious Freedom Award sun kasance 'yan kasashen Sudan, Iraq, Brazil da kuma Cyprus.

Ga wasu al'amura game da gwarzo Imam Abubakar da ya kamata ku sani:

  • An haifi Imam Abubakar cikin garin Bauchi a shekarar 1936. Ya yi rayuwa ta tsawon shekaru 60 a garin Nghar.
  • Shi ne jagoran al'ummar musulmi a wani masallaci da aka gina a alkaryar da mabiya addini Kirista suka tanada.
  • An bayyana shi a cikin jerin mutanen da za su samu kyautar shekara ta masu nuna karfin hali wajen karrama bil Adama ba tare da la'akari da sabanin akidar addini ba.
  • Imam Abubakar wanda ya kasance Bahaushe a dabi'a, harshe da kuma al'ada, shi ne babban limamin kauyen Yelwan Gindi Akwati a karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato.
  • Tare da na'ibin sa wanda ya kasance Bafulatani, Umar Abdullahi, sun tseratar da rayuwar fiye da kiristoci 200 yayin da 'yan daban daji suka yi yunkurin kai masu hari na halaka.
  • An samu rahoton aukuwar wannan mummunan hari a ranar 23 ga watan Yunin 2018 cikin kauyukan Yelwan Gindi Akwati, Swei da Nghar wanda dukkanin su ke karkashin karamar hukumar Barikin Ladi a jihar ta Filato.

KARANTA KUMA: Borris Johnson ya sallami ministan kudin Birtaniya

  • A wannan rana da aka auna tsautsayi bayan kammala jagorancin sallar Azahar, Imamu Abubakar ya boye kiristoci 262 a cikin masallaci da kuma gidansa yayin da suka fito daga cikin duhun daji gadan gadan suna neman mafaka.
  • Babban limamin ya kubutar da kiristoci 262 daga halaka wadanda suka fito daga yankin Berom yayin da makiyaya suka zartar da munanan hare-hare cikin kauyuka goma dake karkashin karamar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel