Za a dauki ma'aikata 8,000 a jihar Zamfara

Za a dauki ma'aikata 8,000 a jihar Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya bayar da sanarwar shirye-shiryen gwamnatin sa na daukar ma'aikata 8,000 domin kara karfin ma'aikatun gwamnatu a jihar.

Sabon gwamnan na Zamfara ya bayyana hakan ne a yayin wani shiri na manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba cikin birnin Gusau. Gwamna Matawalle ya ce tuni gwamnatin sa ta yi tanadin albashin watanni biyar da za ta biya ma'aikatan.

Kazalika gwamnan ya ce gwamnatin sa tayi tanadin kimanin Naira miliyan 150 da za ta rarrabawa fiye da mata 7500 a matsayin hannayen jari da zai zama tallafi a gare su na dogaro da kai.

A wani rahoton na daban da jaridar Legit.ng ta ruwaito, wasu gwamnonin yankin Arewa maso Yammacin Najeriya a ranar Alhamis, za su gudanar da muhimmin taro domin tumke damarar inganta sha'anin matsalar tsaro da ya yiwa jihohin su dabaibayi.

KARANTA KUMA: A yanzu matasa sun fara koyi dani - Sanata Abbo

Gwamnonin jihohin da za su halarci wannan taro a jihar Katsina sun hadar na Zamfara, Katsina, Aminu Bello Masara, na Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da kuma Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.

Har wa yau ta'addanci na ci gaba da ta'azzara a jihohin Arewa maso Yamma kama daga na 'yan daban daji, fashi da makami, masu satar shanu da kuma masu garkuwa da mutane.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel