An cafke masu garkuwa da mutane 5 a jihar Katsina

An cafke masu garkuwa da mutane 5 a jihar Katsina

Rundunar 'yan sandan Najeriya mai yaki da ta'addancin fashi da makami reshen jihar Katsina, ta warware shirin wasu masu ta'adar garkuwa da mutane shida a yayin yunkurin karbar kudin fansa na naira miliyan 15 na wata uwargida, Hajiya Habiba.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, hukumar 'yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar cafke 'yan ta'adda biyar daga cikin shidan da suka yi yunkurin aikata wannan mummunan fasadi.

Masu laifin sun hadar da Abdurrahman Hashimu, Umar Sada, Isiyaku Ya'u, Ado Nasiru da kuma Abdurrahman Mamuda. Na shidan su, Adda'u Lawal ya yi layar zana sai dai hukumar 'yan sandan ta bayar da tabbacin damko shi a yayin da ta bazama wurin bincike.

Rahotanni sun bayyana cewa, ababen zargin shida sun tsallaka gidan Hajiya Habiya dake kauyen Yar'Liyau inda suka yi awon gaba da ita bayan yashe mata dukiya ta kimanin naira 52,700.

Dubunsu ce ta cika a yayin da rundunar 'yan sandan Katsina ta yi masu kwanton bauna cikin wani gida a kauyen 'Yar Magaji dake karamar hukumar Batagarawa inda Hajiya Habiba ke tsare a hannun miyagu.

KARANTA KUMA: Kiwon Lafiya: Amfani 15 na 'baure ga lafiyar dan Adam

A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira da a daina zargin gwamnati da rashin tsaro a Najeriya illa iyaka yaki ne na mu duka da ya kamata kowa ya bayar da tasa gudunmuwar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel