Sojoji sun cafke 'yan daban daji 17 a jihar Katsina

Sojoji sun cafke 'yan daban daji 17 a jihar Katsina

'Yan daban daji kimanin 17 sun afka tarkon rundunar dakarun sojin kasa ta Najeriya, yayin da rayuwar daya daga cikin 'yan ta'addan ta salwanta biyo bayan wani simame na sharar daji da dakaru suka kai a jihar Katsina.

Kalaman wannan babbar nasara da rundunar soji ta samu na zuwa ne a ranar Lahadi cikin wata sanarwa da mataimakin kakakin rundunar sojin, Muhammad Isa Yahaya ya gabatar yayin ganawa da manema labarai.

Katsina na daya daga cikin jihohin da suka fi fama da kalubalen tsaro a Arewacin Najeriya, musamman matsalolin hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu.

Makonni biyu da suka gabata, 'yan bindiga kimanin 300 sun far wa kauyuka uku na Kirtawa, Kinfau da kuma Zamfarawan Madogara da ke yankunan kananan hukumomin Safana da Batsari na jihar Katsina.

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Abubakar Yari, ya ce an sha yin sasanci da 'yan daban daji amma hakan bai kawo karshen ta'addanci ba a jihar.

KARANTA KUMA: Sanata Marafa ya jagoranci addu'o'in samun zaman lafiya a jihar Zamfara

Furucin tsohon gwamnan na zuwa ne yayin bayyana matsayarsa a kan hanyoyin da sabuwar gwamnatin PDP ta Bello Matawalle ta bijiro da ita domin kawo karshen zubar jinin da aka shafe tsawon shekaru ana kokarin magancewa ta hanyar sulhu da wadanda suka jefa jihar cikin halin da ta tsinci kanta a ciki.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel