'Yadda 'Yan Yahoo Suka Kwashe N7.2m daga Asusun Alkali'
- Masu aikata damfarar intanet wanda aka fi sani da 'yan Yahoo sun taba yashe kudaden wata alkalin kotu a tsakar dare
- Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana yadda lamarin ya kasance, yayin ya ke sukar ayyukan 'yan Yahoo
- Ola Olukoyede ya nuna muhimmancin da ke akwai na yin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki yaki da matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Mista Ola Olukayode, ya soki masu ayyukan damfarar intanet da aka fi sani da "Yahoo Boys".
Shugaban na EFCC, Ola Olukoyede ya bayyana yadda aka kwashe sama da Naira miliyan 7.2 daga asusun wata mai shari'a t a tsakar dare.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron kaddamar da wasu littattafai guda biyu da mai shari'a mai ritaya na babbar kotu, Alaba Omolaye-Ajileye ya wallafa.

Kara karanta wannan
Yadda sojoji suka fatattaki 'yan ta'adda da suka kai hari sansanin sojojin Zamfara
Yadda aka yashe kudin mai shari'a
Shugaban na EFCC ya ce an tashe shi daga barci da misalin karfe 1:00 na dare ta hanyar kiran gaggawa da ya samu daga wata mai shari'a a daya daga cikin jihohin Kudu maso Kudu wadda ta fada komar ’yan damfara.
“Mene ne matsalar? An riga an damfare ta kudaden da ta shafe shekaru shida tana tarawa domin tura danta makaranta."
“Ta ce sakonnin cire kudi ne suka tashe ta a barci. Ta rika samun sakonnin cire kudi a daidai wannan lokaci na dare. Shin bankin ne ke aiki, ko kuwa me ke faruwa?"
“Kafin ta ankara, an damfare ta kusan Naira miliyan 7.2. Don haka ta bugo mini waya cewa dole ne na dauki mataki."
“Wani abin mamaki kuma, jihar ita ce inda aka taba samun umarnin kotu na hana EFCC binciken wasu laifuffuka. Kuma na ce, ‘mai shari'a ina da umarni, wato takardar hana binciken laifuffukan kudi a wannan jihar.’"
“Ta ce, ‘A’a, a’a, a’a! Wannan ya fita daban. Dole ne ku yi wani abu cikin gaggawa!’"
"Kuna fahimtar gabar da nake son nunawa a nan? Idan ka zama wanda abin ya shafa kai tsaye, a lokacin ne za ka gane cewa lallai akwai bukatar a yi wani abu."
- Ola Olukoyede
EFCC ta kwato kudi daga hannun 'yan Yahoo
Shugaban na hukumar EFCC ya ci gaba da cewa:
"Kafin karfe 6:00 na yamma, mun kwato mata dukkan kudin. Na tabbata cewa idan aka kawo wata bukata a gabanta, ya mai shari'a ta neman a hana EFCC gudanar da ayyukanta, za ta yi fatali da ita saboda ita ma ta zama wacce abin ya shafa."
“Don haka, yana da mahimmanci mu fahimci zurfin wannan matsalar.”

Source: Facebook
Shugaban na EFCC ya ce akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki da abin ya shafa domin karfafa yaki da laifuffukan kudi a kasar, rahoton Daily Post ya nuna hakan.
EFCC ta kai tsofaffin shugabannin matatu kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa EFCC ta gurfanar da tsofaffin shugabannin PHRC da WRPC kan zargin karkatar da kudaden gyaran matatun man fetur da halasta kudaden haram.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawar ta shigar da tuhume-tuhume 12 kan Ahmed Dikko da kuma 8 kan Jimoh Yisawu a wata kotun Abuja.
EFCC ta gurfanar da mutanen biyu ne kan zargin halasta kudaden haram da suka shafi kudaden gyaran matatun mai na Najeriya.
Asali: Legit.ng

