Kwankwaso ya yi magana kan tsagewar gadar da ya gina kan miliyan 700 a Kano

Kwankwaso ya yi magana kan tsagewar gadar da ya gina kan miliyan 700 a Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ba gwamnatinsa bane ta gina bangaren gadar Abubakar Audu da ke hanyar BUK daura da Gadon Kaya ta da fara tsagewa.

Martanin da tsohon gwamnan ya yi a ranar Juma'a na dauke cikin wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri kuma dan takarar gwamnan PDP na jihar Kano a 2019, Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.

Wata kafar yada labarai na Intanet, Kano Today ta ruwaito cewa gadan ta tsage ne bayan wani ruwan zama da kaman bakin kwarya da aka yi a jihar a yammacin ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: An kama tsohon dan majalisa bisa zargin safarar bindigu da garkuwa da mutane

Sanarwar ta ce gwamnatin Ganduje ne tayi gyaran titin da ta hade Gadon Kaya da Yahaya road, da gefen Hauren Legal da kuma U-turn zuwa Kofar Gadon Kaya city gate da sabuwar hanyar da ta fito daga Hauren Shanu zuwa Kofar Gadon Kaya.

Ta ce gwamnatin Kwankwaso da ta gina gadan ba ta kara yin wani gini a jikin gadar ba kafin mika mulki a Mayun shekarar 2015.

Har ila yau, sanarwar ta yi ikirarin cewa kwararru a fanin gine-gine sun san cewa ba ayi aikin kan ka'ida ba saboda kawai ana neman filin da za a gina kananan shaguna a kusa da gadan wanda hakan ya sabawa tsarin babban gada irin wannan.

Sanarwar ta ce, "Idan al'umma ba su manta ba irin wannan tsagewar gadan ta faru a shekarar 2018 a wurare da dama a gefen gadar Kofar Ruwa da gwamnatin Ganduje ta gina.

"Hakan na cikin kura-kuren da suke yi saboda ba su dauko kwararru da suka iya aiki, suna aiki da baragulbin ma'aikata ne saboda su karkatar da kudin al'umma zuwa aljihunansu."

Sanarwar ta kuma ce kudin da aka kashe wurin gina gadar Prince Audu Abubakar bai kai naira miliyan 700 ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke bayyana wa sai dai idan gwamnati mai ci yanzu ta sake bitan kasafin kudin da aka kashe wurin gina gadan ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel