Sauran kiris ta'addancin 'yan daban daji ya zama tarihi a jihar Katsina - Masari
Cikin karsashi na bayyana farin ciki da kyautata zato, gwamnan jihar Kastina Aminu Bello Masari, ya yi karin haske da cewar ba tare da daukar wani lokaci mai tsawo ba rashin tsaro da ta'addancin 'yan daban daji zai zamto tarihi a jihar.
Gwamnan yayin bayyana gamsuwar sa, ya zayyana wannan furuci a sanadiyar yadda hukumomin tsaro, gwamnatin jihar da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki suka daura damarar tunkarar wannan annoba da yiwa jihar dauri na dabaibayi.
Furucin Masari ya zo ne bayan ganawar sa ta tsawon awanni biyar da fadar gwamnatin sa tare da shugabannin hukumomin tsaro na jihar, babban sakataren gwamnatin sa, da kuma manyan sarakuna na garin Daura da kuma Katsina.
Yayin ganawar su, sun yi itifakin cewa babu shakka an samu inganci na harkokin tsaro musamman a kananan hukumomin takwas na jihar da annobar ta'addanci ta fi ciwa tuwo a kwarya.
Dangane da bayar da kariya ga manoma, gwamna Masari ya ce tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma ita ce ka-in-da-la-in ta gwamnatin sa a yanzu gabanin karkatar da akalar sa ta mayar da hankali a kan sauran kalubale musamman bayar da kariya ga manoma da zai biyo baya.
KARANTA KUMA: Za mu yi tsanani wajen karbar kudin shiga a jihar Kano - Ganduje
A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito a watan Mayun da ya gabata, gwamnan Masari ya nem jama'a da su daina biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa wajen neman kubutar da 'yan uwan su.
Hakazalika, gwamnatin jihar Katsina a kwanan baya ta bayyana cewa masu garkuwa da mutane da barayin shanu za su rika fuskantar hukuncin kisa a duk sa'ilin da aka same su da laifi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng