Arewa Ta Fara Farfadowa, an Bude Babban Kamfanin Lithium a Nasarawa

Arewa Ta Fara Farfadowa, an Bude Babban Kamfanin Lithium a Nasarawa

  • Sanata Kashim Shettima ya ƙaddamar da babbar masana’antar sarrafa ma’adinin lithium mafi girma a Najeriya a jihar Nasarawa
  • Gwamnatin tarayya ta ce tana son Najeriya ta daina fitar da ma’adanai ketare, ta tana so a dawo sarrafa su a cikin kasa
  • A bayanin da ya yi, Shettima ya ce sauye-sauyen tattalin arziƙi da Bola Tinubu ya yi sun ƙara jawo masu zuba jari Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da babbar masana’antar sarrafa ma’adinin lithium mafi girma a Najeriya da ke jihar Nasarawa.

Shettima ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin mayar da ƙasar babba a fannin tattalin arziƙin ma’adanai ta hanyar ƙara masu ƙima, samar da ayyukan yi da bunƙasa masana’antu.

Kara karanta wannan

Dan a mutun Tinubu ya kare Oluremi, ya ba da labarin attajira mai sayar da ƙosai a Abuja

Kamfanin jihar Nasarawa
Babban kamfanin lithium da aka yi a Nasarawa. Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kashim Shettima ya sanar da cewa ya wakilci shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen ƙaddamar da masana’antar

Bayanin Sanata Kashim Shettima

Yayin da ya ke bayani a wajen, Kashim Shettima ya ce ɓangaren ma’adanai ya zama muhimmin ginshiƙi a shirin gwamnatin na sauya fasalin tattalin arziƙi.

Ya ce dole Najeriya ta yi amfani da dimbin albarkatun ma’adananta ta hanyar daina fitar da su kai tsaye zuwa ƙasashen waje, tare da mayar da hankali kan sarrafa su domin samar da ayyukan yi, haɓaka ƙwarewar ma’aikata da faɗaɗa tattalin arziƙin ƙasa.

Shettima ya ce dimbin ma’adanan lithium, zinariya, tin, baƙin ƙarfe, kwal da sauran muhimman ma’adanai da Najeriya ke da su ba za su amfani al'umma ba sai an yi amfani da su wajen bunƙasa masana’antu da inganta rayuwar 'yan ƙasa.

Ya ce Najeriya na da zaɓi biyu, ko dai ta yi amfani da damar da albarkatun ƙasarta wajen samar da ci gaba, ko kuma ta ci gaba da neman uzuri tana zama kurar baya.

Kara karanta wannan

Tinubu zai dauki matasa 5,000 domin ba su horo su samu sana'a

Kashim Shettima a kamfanin Nasarawa
Kashim Shettima tare da manyan baki a kamfanin da da aka yi a Nasarawa.
Source: Facebook

Tasirin kamfanin ga Najeriya

Shettima ya ce ƙaddamar da wannan masana’anta alama ce da ke nuna yadda masu zuba jari ke ƙara amincewa da Najeriya da jihar Nasarawa, da kuma sauye-sauyen tattalin arziƙin da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.

Ya ƙara da cewa masana’antar na nuna cewa Najeriya ta shirya shiga kasuwar ma’adanai ta duniya ta hanyar da za ta samar da ayyukan yi, bunƙasa ƙwarewa, ƙarfafa kamfanonin cikin gida da kuma faɗaɗa ƙarfin samar da kayayyaki.

A cewarsa, tattaunawa kan arzikin ma’adanan Najeriya ba za ta haifar da wani amfani ba sai ƙasar ta mayar da albarkatun ƙasarta zuwa kayayyakin da aka sarrafa domin haɓaka tattalin arziƙi.

An kaddamar da titi a Nasarawa

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da aikin titi a Akwanga da ke jihar Nasarawa.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da ya wakilci shugaba Bola Tinubu ya ce aikin zai farfado da jihohin da ya shafa.

Ministan ayyuka, Dave Umahi, Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, shugaban gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng