An Sanya Lokaci: Za a Gurfanar da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
- Babbar kotun jihar Kwara ta sanya ranar gurfanar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, kan zargin bata sunan gwamna
- Gwamnatin Kwara ta zargi Saraki da wallafa kalaman cin mutunci da ƙarya, da ya ce gwamnan jihar bai kai matakin karatun sakandare ba
- Kotun ta yi watsi da ƙorafin lauyoyin Saraki kan rashin hurumi da sauran buƙatunsu, tana mai cewa shari'ar tana ƙarƙashin ikonta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kwara – Babbar kotun jihar Kwara da ke zamanta a Ilorin ta sanya ranar 22 ga Yulin 2026 domin gurfanar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
Za a gurfanar da tsohon shugaban majalisar ne kan zargin yin kalaman bata suna da cin mutuncin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.

Source: Twitter
Gwamnatin jihar Kwara ce ta shigar da ƙarar, tana zargin Saraki da aikata laifin bata suna ta hanyar wallafa wasu kalamai a kafafen sada zumunta da kuma jaridu, in ji rahoton Channels TV.
Zargin da gwamnatin Kwara ke yi wa Saraki
A cewar gwamnatin jihar, Saraki ya wallafa wata sanarwa a ranar 17 ga Afrilu, 2026, inda ya yi iƙirarin cewa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq bai kai matakin karatun sakandare ba.
Ta ce kalaman sun ƙunshi cin mutunci da zagi, kuma Saraki ya san ko ya kamata ya san cewa bayanan ba gaskiya ba ne.
Haka kuma gwamnatin ta ce an wallafa kalaman ne da niyyar tunzura gwamnan da gwamnatin jihar, abin da ka iya haddasa hargitsi da tada zaune tsaye a tsakanin al'umma.
Lauyoyin Saraki sun nemi a soke shari'ar
Jaridar Punch ta rahoto lauyan Saraki, Jimoh Mumeen (SAN), ya roƙi kotu ta yi watsi da shari'ar, yana mai cewa kotun ba ta da hurumin sauraron ta.
Ya kuma yi zargin cewa ba a bi ƙa'idojin shigar da ƙarar yadda ya kamata ba, tare da cewa shari'ar ba ta dace a saurare ta a babbar kotun jihar ba.
Sai dai lauyan gwamnatin jihar, Rafiu Balogun, ya buƙaci kotu ta yi watsi da wannan ƙorafi, yana mai cewa buƙatun Saraki ba su da tushe.

Source: Original
Kotun ta yi watsi da ƙorafin Saraki
A hukuncin da ya yanke, Mai Shari'a M.O. Folorunsho ya yi watsi da dukkan buƙatun da Saraki ya gabatar.
Ya ce kotun tana da cikakken hurumin sauraron shari'ar, kuma tuhumar bata suna da ake yi wa Saraki tana nan daram.
Alƙalin ya kuma bayyana cewa babu wata alama da ke nuna cewa shari'ar tana da alaƙa da siyasa.
Daga nan ne kotun ta ɗage shari'ar zuwa 22 ga Yulin 2026, ranar da za a gurfanar da Bukola Saraki a gaban kotu.
Saraki da tsohon gwamna za su gurfana
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki, da tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatai Ahmed, za su fuskanci sabbin tuhume-tuhume guda 20.
Tuhume-tuhumen sun shafi kisan kai, haɗin baki wajen aikata laifi, da sauran laifuffuka da gwamnatin jihar Kwara ta shigar a kansu game da mummunan fashin bankin Offa na shekarar 2018.
Masu shigar da ƙara sun yi zargin cewa waɗanda ake ƙarar sun haɗa baki wajen ɗaukar nauyi da samar wa wasu mutane makamai da ke da alaƙa da mummunan fashin.
Asali: Legit.ng

