'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 4 a Taraba

'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 4 a Taraba

Mutane hudu masu ta'adar garkuwa da mutane sun yi gamo da fushin hukumar tsaro yayin da jami'an 'yan sanda suka salwantar da rayukan su a karamar hukumar Bali ta jihar Taraba dake Arewa maso Gabashin Najeriya.

Wannan nasara na zuwa ne bayan mako guda da hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Taraba ta kaddamar da wani sabon shiri na daurin damar a kan tsananta matakan tsaro domin yakar ta'addanci garkuwa da mutane tare da hadin gwiwar rassan jami'an tsaro masu yakar fashi da makami.

Hukumar 'yan sanda ta kaddamar da wani shiri tare da hadin gwiwar 'yan sintiri daga kauyen Kungana a karamar ta Bali kamar yadda jaridar vanguard ta ruwaito.

Da yake bayar da tabbacin wannan rahoto yayin ganawa da manema labarai ta hanyar wayar tarho, kakakin rundunar 'yan sandan jihar DSP David Misal, ya ce masu ta'adar garkuwa da mutane sun yi gamo da azal yayin da jami'an tsaro suka tarwatsa wani sansanin sa dake saman dutse.

KARANTA KUMA: Buhari ya yi Allah wadai kan harin da aka kaiwa masu jana'iza a Borno

Ya kuma bayar da shaidar cewa, an samu nasarar cafke miyagun makamai kama daga bindigu da kuma sauran kayan yaki daban-daban, layu da kuma tukwane a sansanin na 'yan ta'dda.

Jaridar BBC Hausa ta ruwaito cewa, ta'addancin masu garkuwa da mutane dai ya zama ruwan dare a Najeriya, inda masu satar mutane ke harar baki 'yan kasashen waje da 'yan Najeriyar musamman masu idanu da tozali.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel