Sabbin Ministocin Buhari daga jihohin Arewa

Sabbin Ministocin Buhari daga jihohin Arewa

Karshen tika-tik kuma komai nisan dare gari zai waye domin kuwa a yau Talata, 23 ga watan Yulin 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da sunayen ministocin sabuwar gwamnatin sa a zauren majalisar dattawa.

A ranar Talata, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana jerin sunayen ministoci 43 da shugaban kasa Buhari ya zaba domin sauke masa wani nauyin al'ummar kasar nan da rataya a wuyan sa.

Bayan tsawon fiye da kwanaki 50 da karbar rantsuwa ta sabuwar gwamnatin sa a wa'adi na biyu da aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayu, shugaban kasa Buhari ya fidda jerin sunayen sabbin ministocin sa tare da neman amincewar majalisar tarayya.

A yayin da ake sa ran gobe majalisar za ta fara tantance sabbin minstocin, mun kawo muku jerin sunayen zababbu daga jihohin Arewa kadai kamar haka:

1. Muhammadu Musa Bello - Adamawa

2. Adamu Adamu - Bauchi

3. Amb Maryam Y. Katagum - Bauchi

4. Mustapha Baba Shehuri - Borno

5. Isa Ali Pantami - Gombe

6. Suleiman H. Adamu - Jigawa

7. Zainab Shamsuna Ahmed - Kaduna

8. Dr. Muhammad Mahmud - Kaduna

9. Sabo Nanono - Kano

10. Maj. Gen (rtd) Bashir Salihi Magashi - Kano

11. Hadi Sirika - Katsina

12. Abubakar Malami - Kebbi

13. Ramatu Tijjani - Kogi

14. Lai Mohammed - Kwara

15. Gbamisola Saraki - Kwara

KARANTA KUMA: Jerin ministoci 13 da suka samu dawowa majalisar Buhari

16. Muhammad H. Abdullahi - Nasarawa

17. Amb. Zubairu Dada - Niger

18. Pauline Tallen - Filato

19. Muhammad Maigari Dingyadi - Sakkwato

20. Eng. Saleh Mamman - Taraba

21. Abubakar D. Aliyu - Yobe

22. Sa'adiya Umar Farouk - Zamfara

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel