Matakai 4 da Aka Dauka kan Kashe Malama Ummulkhairi da Mutane Suka yi a Kaduna

Matakai 4 da Aka Dauka kan Kashe Malama Ummulkhairi da Mutane Suka yi a Kaduna

Kaduna, Nigeria - A ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, 2026 wasu gungun mutane suka dauki doka a hannu ta hanyar kashe malamar Islamiyya mai suna Ummulkhairi Usman Aliyu a garin Maraban Jos da ke jihar Kaduna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayanai sun nuna cewa mutanen sun kashe matar ne bisa zarginta da satar kananun yara, lamarin da daga bisani aka tabbatar da ba gaskiya ba ne.

Kaduna.
Wurin da aka kashe tare da kona gawar Malama Ummulkhairi da kwamishinan yan sandan Kaduna Hoto: Mansur Hassan
Source: Facebook

Rundunar yan sandan Kaduna ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, 22 ga Yuni, 2026, kamar yadda tashar NTA News ta wallafa a shafinta na Facebook.

Yadda aka kashe Malama Ummulkhairi Usman

Mai magana da yawun rundunar, Mansur Hassan, ya bayyana cewa da misalin karfe 10:00 na safe suka samu labarin lamarin, kuma nan take aka tura jami'an tsaro na caji ofis din Maraban Jos.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa masu koyon karatun Alkur'ani wuta a Bauchi

Sai dai rahoton 'yan sanda ya nuna cewa bayan an kawo Malama Ummulkhairi caji ofis na Maraban Jos, matasa maza da mata sun ƙwace ta daga hannun jami'an tsaro, sannan suka kashe ta.

Wannan mummunan al'amari dai ya ja hankali matuka, musamman yadda gungun mutane suka kona malamar da ranta a gaban ofishin 'yan sanda.

Bayanai sun nuna cewa mai garin Sabon Maraban Jos, Suleiman Isa, da malamin su Ummulkhairi sun yi iya bakin kokarinsu wajen jan hankalin mutane su bari doka ta yi aikinta, amma hakan bai yi aiki ba.

Matakan da aka dauka bayan kisan

Bayan faruwar lamarin, rundunar 'yan sandan Najeriya da gwamnatin jihar Kaduna sun sha alwashin hukunta duk wanda ke da hannu a aikata wannan danyen aiki.

Sakamakon haka, Legit Hausa ta tattaro matakai hudu da hukumomi suka dauka zuwa yanzu, da nufin tabbatar da an yi wa marigayiya Ummulkhairi adalci. Ga su kamar haka:

1. An kama fiye da mutane 100

Bayan abin da ya faru, rundunar 'yan sandan Najeriya ta fara bincike tare da alkawarin kama duk wadanda ake zargi sun taimaka wajen kashe Malama Ummulkhairi a Maraban Jos.

Kara karanta wannan

DSS da yan sanda sun yi bincike, an ji gaskiya kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta'addanci a Najeriya

A wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, Mansir Hassan ya tabbatar da cewa dakaru sun cafke mutane sama da 100 kuma ana ci gaba da bincike a kansu.

Yan sanda.
Dakarun rundunar 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: PoliceNG
Source: Twitter

Ya ba da tabbacin cewa duk wanda aka gano yana da hannu a kisan, za a gurfanar da shi a gaban kotu domin ya girbi abin da ya shuka.

Kwamishinan ‘yan sandan Kaduna, Muhammad Rabiu, ya kwantar da hankulan jama’a, yana mai cewa cewa za a tabbatar da adalci tare da ci gaba da kare doka da oda a fadin jihar.

2. Umarnin bincikar DPO

Wasu rahotanni da ke yawo sun zargi DPO na ofishin yan sandan Maraban Jos da taimaka wa wajen aikata wannan mummunan laifi.

Ana zargin shugaban caji ofis din da mika malamar ga fusatattun mutane, lamarin da rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne.

Bayan korafin da aka shigar kan DPO, rundunar 'yan sandan Najeriya ta bukaci a binciki jami'in ta da ake zargi ya yi sakaci game da lamarin.

Disu.
Sufeton Yan Sandan Najeriya, IGP Tunji Disu da marigayiya Malama Ummulkhairi Usman Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Lauya mai kare hakkin dan Adam, Barista Hamza Nuhu Dantani ya wallafa a Facebook cewa ya gana da sufeton 'yan sanda game da zargin da aka yi wa DPO da ke lura da caji ofis din da abin ya faru.

Kara karanta wannan

Allah Ya ceci wani mutumi da matarsa ta lallaba za ta yanka masa wuya yana barci a Katsina

"Sufeton 'yan sanda, IGP Disu Tunji, ya bada umurnin gaggawa na a binciki hakikanin abin da ya sa DPO ya mika matar ga jama'a har ya kai ga mutuwarta," in ji shi.

3. An gurfanar da mutane 36 a kotu

A karon farko bayan gudanar da bincike kan waɗanda aka kama, yan sanda sun gurfanar da mutane 24 a gaban kotun majistare da ke NDA Junction, Kaduna, bisa zargin hannu a kisan Malama Ummulkhairi.

Awanni 24 bayan haka, rundunar 'yan sandan ta sanar cewa ta gurfanar da karin mutum 17 saboda bincike ya nuna da hannunsu a kisan malamar Islamiyya, kamar yadda tashar Channels TV ta rahoto.

Uba Sani.
Gwamna Uba Sani yana magana da yan jarida yayin da ya kai ziyara gidan marigayiya Ummulkhairi Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

An tuhumi wadanda ake zargin da hada baki wajen aikata laifi, tayar da zaune tsaye, barna, lalata kadarorin gwamnati da na ‘yan sanda, da kuma kisan kai.

4. Ɗaukar nauyin iyalanta

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta dauki nauyin karatun 'ya'yan marigayiya Ummulkhairi, wacce mutane suka kashe a Maraban Jos.

Malam Uba Sani ya sanar da haka ne a lokacin da ya ziyarci iyalan malamar domin jajanta masu da kuma ta'aziyyar wannan rashi da suka yi, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Amurka ta samu nasara mafi girma cikin shekaru 25 a farmakin da ta kawo Najeriya

Gwamnan ya kuma tabbatar wa mijin ta, Malam Aliyu da sauran yan uwa da ya hadu da su cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen kamo masu hannu a lamarin tare da gurfanar da su a kotu.

“Mun kuma yi alƙawari ga Malam Aliyu cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta ɗauki nauyin karatu da jin daɗin yaran da Ummulkhairi ta bari," in ji Gwamna Uba Sani.
Gwamna Uba Sani.
Gwamna Uba Sani tare da 'ya'yan Malama Ummulkhairi lokacin da ya je ta'aziyya Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

An tallafawa iyalan Ummulkhairi

A wani rahoton, kun ji cewa malaman Islamiyya a sassan Najeriya sun hada kudi domin tallafawa iyalan malamar Islamiyya da aka kashe bisa zargin satar yara a Kaduna.

A ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin 2026 ustazan suka tura tawaga ta musamman da kudi domin tallafawa 'ya'yan da Malama Ummulkhairi ta bari a duniya.

Rahotanni sun nuna cewa malaman Islamiyya sun hada kudi sama da N200,000 domin ba iyalan marigayiyar su rage wasu dawainiyoyyin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262