Boko Haram ta kashe mutane da dama a harin da ta kai a Jakana

Boko Haram ta kashe mutane da dama a harin da ta kai a Jakana

'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai hari a kauyen Jakana da ke karamar hukumar Konduga na jihar Borno a daren jiya kamar yadda wasu jami'an tsaro na sa kai tabbatar.

An ce harin ya faru ne misalin karfe 6.30 na yamma a kan titin Maiduguri zuwa Kano.

'Yan ta'addan sun iso cikin motocci masu dauke da bindigu 6 inda suka rika harbe-harbe ba kakautawa.

Rahotanni sun ce 'yan ta'addan sun sace kayayyakin abinci masu yawa.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Gwamna Ganduje ya yi sabbin nade-nade 9

Wata majiya ta ce babu Sojoji ko 'Yan sanda a kauyen a yayin da 'yan ta'addan suka kai hari domin an janye sojojin da 'Yan sandan kwanaki biyu da suka shude.

Wani mazaunin garin, Babagana Adam ya shaidawa Daily Trust cewa 'yan ta'addan sun iso kauyen cikin motoccin yaki irin na sojoji guda 6 masu dauke da bindigu.

"Munyi tsamanin sojojin suka dawo domin shigar da su kayi tayi kama da na sojoji har sai da sika fara ihu suna cewa 'Allah Akbar' sannan mutane suka fara tserewa. Daga bisani suka rika balle shaguna suna diban kayan masarufi da kayan abinci.

"Ban san adadin mutanen da suka mutu ba amma tabbas akwai yiwuwar mutane da dama sun mutu saboda yadda 'yan ta'addan suka rika yin barin wuta. A halin yanzu ina kan bishiya ne kuma yara da dama ba su san inda iyayensu suke ba. Muna bukatar taimako," inji Adam.

Sai dai wata majiyar tsaro ta ce: "A yanzu da muke magana sojoji suna Jakana kuma suna fafatawa da 'yan ta'addan; ragwaya ne ('yan ta'addan)."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel