Sanata Marafa ya jagoranci addu'o'in samun zaman lafiya a jihar Zamfara

Sanata Marafa ya jagoranci addu'o'in samun zaman lafiya a jihar Zamfara

Wasu mambobin kungiyar jam'iyya mai mulki ta APC wadda ake yiwa lakabi da G8, a ranar Lahadi sun bayyana goyon bayansu a kan irin kokarin da gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ke yi wajen tafiyar da al'amuran gwamnatinsa, domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Kungiyar wadda har wayau ta jagoranci zaman gudanar da addu'o'i na musamman a birnin Gusau domin samuwar kwanciyar hankali gami da ingataccen tsaro, ta ce tana kuma goyon bayan zaman neman sulhu da 'yan daban daji wanda gwamnatin Matawalle ke ci gaba da aiwatarwa.

A kalaman wakilin Sanata Kabiru Marafa yayin taron gudanar da addu'o'i wanda kuma ya kasance shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara, Alhaji Surajo Mai Katako, ya ce su na ci gaba da goyon bayan yadda gwamnatin Matawalle ke riko da akalar jagoranci.

Alhaji Mai Katako ya yi kira na neman gwamna Matawalle da ya gaggauta fara gudanar da bincike a kan tsohuwar gwamnatin jihar ta Abdulaziz Abubakar Yari, domin dawo da duk wata dukiyar da ta wawushe.

KARANTA KUMA: Sojoji sun kashe 'yan daban daji 5 a Kaduna

Kazalika Rabi'u Sulaiman wanda ya wakilci tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mallam Ibragim Muhammad Wakkala, ya kira yi dukkanin 'ya'yan kungiyar da su shimfida goyon bayan a kan gwamna Matawalle tare da kara masa karfin gwiwa ta fidda jihar zuwa tudun mun tsira.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel