Hatsari a Maigatari: Rayuka 7 sun salwata, Mutane 11 sun jikkata a Jigawa

Hatsari a Maigatari: Rayuka 7 sun salwata, Mutane 11 sun jikkata a Jigawa

Kimanin rayukan mutane 7 ne suka salwanta yayin da wani mummunan hatsarin mota ya auku a a kan wata babbar hanya a kauyen Kwalande dake karamar hukumar Maigatari a jihar Jigawa dake Arewa maso Yammacin Najeriya.

Hatsarin ya auku a tsakanin wasu motoci biyu kirar Peugot 206 da kuma Golf 3 kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

SP Abdu Jinjiri, kakakin hukumar 'yan sandan jihar Jigawa, shi ne ya bayar da tabbacin wannan sanarwa yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Dutse a ranar Litinin.

Aukuwar wannan mummunan hatsari da misalin karfe 1.30 na ranar Lahadi 28 ga watan Yuli, ya salwantar da rayukan mutane bakwai nan take yayin da mutane 11 da suka hadar da direbobin motocin biyu suka jikkata.

KARANTA KUMA: Aikin Hajji: Maniyyatan Najeriya 24,993 daga jihohi 21 sun isa kasar Saudiya

An garzaya da wadanda suka jikkata tare da killace gawar wadanda suka riga mu gidan gaskiya a babban asibitin garin Gumel dake karamar hukumar Gumel a jihar Jigawa.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, wannan mummunan hatsari ya auku a yayin da motocin biyu suka ci karo gami da gwabzawa junan su.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel