Yadda Dannau Ya Danne 'Yan Bindiga a Barci, Wanda Suka Sace Suka Gudu
- Rahoto ya nuna cewa mutum 11 da aka yi garkuwa da su a gonakinsu a jihar Edo sun tsere bayan masu garkuwar sun yi barci
- Wata daga cikin mutanen da aka sace ta ce mijinta ya biya har Naira miliyan 3 tare da ƙarin N300,000 kafin 'yan ta'addan su sake ta
- Bugu da kari, rundunar 'yan sandan jihar Edo ta ce ta kama mutane 32 da ake zargi masu garkuwa da mutane ne a Yunin 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Mutane 11 da aka yi garkuwa da su yayin da suke aiki a gonakinsu da ke Ƙaramar Hukumar Estako ta Yamma a Jihar Edo sun tsere.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa sun gudu ne bayan masu garkuwar sun yi barci saboda gajiyar tafiyar da suka yi da su cikin daji tsawon dare.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa masu koyon karatun Alkur'ani wuta a Bauchi

Source: Original
Bayanin wanda aka sace
Da yake magana a hedikwatar 'yan sanda, Braimah Destiny, wanda ya yi magana a madadin sauran waɗanda aka ceto, Punch ta rahoto ya ce yana dawowa daga gona ne lokacin da ya ci karo da mutane shida da da bindigogi da adduna.
Ya ce masu garkuwar sun sace shi tare da wasu mutum 10, sannan suka tafi da su cikin daji, inda suka riƙa jin karar harbe-harben 'yan sanda yayin da ake tafiya da su.
A cewarsa, sun yi tafiya cikin dare, sannan bayan masu garkuwar sun kai su wani wuri suka ɓoye, saboda gajiya suka yi barci, lamarin da ya ba su damar tserewa zuwa wajen 'yan sanda.
Matatar da aka sace ta magantu
Wata daga cikin waɗanda aka sace, Gloria Inyanugbo, ta ce ta shafe kwanaki huɗu a hannun masu garkuwar kafin mijinta ya biya Naira miliyan 3, tare da ƙarin N300,000 domin sayen miyagun ƙwayoyi da sauransu.
Ta ce masu sa-kai sun kama biyu daga cikin masu garkuwar a cikin daji, yayin da 'yan sanda suka kama wasu ta hanyar amfani da bayanan bincike da fasahar bibiyar wayoyi.
An kama masu garkuwa
A wani ɓangare kuma, rundunar 'yan sandan jihar Edo ta bayyana cewa ta kama mutane 32 da ake zargi da garkuwa da mutane a cikin watan Yuni.
Leadership ta rahoto cewa rundunar ta ce ta ceto mutum 38 da aka yi garkuwa da su ta hanyar ayyukan leƙen asiri da kuma haɗin gwiwar jami'an tsaro.

Source: Twitter
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Monday Agbonika, ya ce rundunar ta kuma kama mutane 15 da ake zargi da ayyukan ƙungiyoyin asiri, mutum uku da ake zargi da fashi da makami da sauransu.
An sace mutane a Sokoto
A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun farmaki wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto.
Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwar sun sace mutane kusan 50 yayin harin, wanda galibin su matan aure ne da yara kanana.
An tabbatar da cewa daga cikin mutanen da aka sace akwai matar limamin garin tare da bindige wani yaro dan shekara 10 da haihuwa.
Asali: Legit.ng
