Sojan sama ya yi tsintuwar €37,000 ya mayar wa da mai su a jihar Kano

Sojan sama ya yi tsintuwar €37,000 ya mayar wa da mai su a jihar Kano

Da yake dai a koda yaushe na gari ba sa karewa duk da dai a wannan zamani sai an tona, mun samu cewa wani karamin ma'aikacin sojan sama na Najeriya, Bashir Umar, ya yi tsintuwar dukiya mai tarin yawa kuma ya mayar wa da mai ita.

Bashir ya yi tsintuwar makudan kudi cikin nau'in su na Tarayyar Turai har Yuro dubu talatin da bakwai (€37,000) a cikin wata 'yar karamar lalita a sansanin Alhazai na jihar Kano kuma ya mayar wa da mai su.

Cikin wata sanarwa da hukumar dakarun sojin saman Najeriya ta fitar a ranar Lahadi, jami'in sojin ya yi kacibus da 'yar karamar jakar cike da zunzurutun kudi tare da wata lambar waya rubuce a jikin wata 'yar takarda yayin da yake rangadi tare da abokanan aiki a ranar Talata.

Bayan kiran wannan lambar waya ta salula, ma'aikacin sojin ya mayar wa da mamallakin wannan dukiya mai sunan Alhaji Ahmad ba tare da daukar masa ko sule ba kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Bill Gates ya yabi jihar Kano a kan yaki da cutar shan inna

Domin ramawa kura kyakkyawar aniyar ta, shugaban hafsin sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya bayar da umurnin yi wa Bashir sakayya ta kwarai domin ya zamto izina ga wadansu kamar yadda kakakin rundunar sojin sama Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyana.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel