Arewa
Kwamadan hukumar NSCDC reshen jihar Neja, Mr George Edem, shi ne ya bayar da tabbacin wannan mummunan rahoto da cewar wanda ake zargi ya aikata laifin ne a kauyen Tamanine na karamar hukumar Borgu a jihar.
Malam Yahaya Yakubu ya ke cewa, kungiyar mu ba ta da wata manufa face tabbatar da ci gaban addini bisa fahimta ta irin ta akidar mu ko ina a fadin duniya, kuma wannan tattakin mun saba gudanar da shi a kowace shekara.
Wani mazaunin gari, Muhammadu Haruna, ya ce yaran da suka riga mu gidan gaskiya sun kasance a kan hanyar su ta komawa gida bayan dawowa daga cin kasuwar Lambatta inda motarsu ta dulmiye cikin ruwa.
Shugaban hukumar NDLEA reshen jihar, Peter Odaudu, yayin zantawa da manema labarai a ranar Juma'a ya bayyana cewa, wannan katafariyar gona ta kasance ta biyu ta fuskar girma wadda a aka gano a tarihin jihar Kebbi.
An alakanta ambaliyar ruwa daga kogin Amba da samun wata karamar hanya da ruwa ke zirarewa. Gadar kogin Amba ta hada kauyuka da dama da hanyar zuwa Doma. Ambaliyar kogin ta jawo tsaiko wajen zirga-zirgar mutanen dake amfani da gad
Direban motar wanda hauragiyar ta auku a sanadiyarsa, Kabiru Muhammad, ya shaidawa manema labari cewa, jami'an hukumar KAROTA sun kai mai cafka da laifin amfani da fitilun mota doriya a kan wadanda motarsa ta zo dasu.
Ana rikici tsakanin wasu Kabilu a Yankin Mokwa da Katcha a Neja. Rigimar wannan Kabilu ta ci mutane a Jihar Neja inda yanzu aka nemi Shugaban kasa ya sa baki a cikin rikicin tun kafin abu ya cabe.
Alhaji Bala ya bayyana takaici gami da damuwa dangane da yadda da yawa daga cikin 'yan kasuwar Arewa suka fada kwatami da kuma samun karayar arziki a sanadiyar muzgunawa ta shugaban hukumar kwastam.
Dattijon arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya jajanta kalubalen da Fulani makiyaya ke fuskanta a Najeriya. Ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya maida hankali akan matsalolin. Ango, tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello da
Arewa
Samu kari