Ambaliya: Mutane 3 sun mutu, da dama sun bata, gidaje sun nitse a Nasarawa

Ambaliya: Mutane 3 sun mutu, da dama sun bata, gidaje sun nitse a Nasarawa

Wata ambaliyar ruwan sama da aka yi tsakar dare sakamakon mamakon ruwan sama a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, ta yi sanadiyar mutuwar mutane uku da lalata gidaje, makabartu da gonaki.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an samu ambaliyar ruwa mai tsanani a sassan birnin Lafiya bayan an shafe sa'o'i masu yawa ana tsuga ruwan sama da daddare.

Wani mazaunin unguwar Filin Kura, Saidu Iliya, ya shaida wa Daily Trust cewa, "an fara ruwan ne da misalin karfe 3:00 na dare, amma kafin karfe 7:00 na safiya gidana ya cika makil da ruwa. Kogin gadar Amba bai taba ambaliya kamar irin ta wannan lokacin ba."

An alakanta ambaliyar ruwa daga kogin Amba da samun wata karamar hanya da ruwa ke zirarewa. Gadar kogin Amba ta hada kauyuka da dama da hanyar zuwa Doma.

DUBA WANNAN: An yanke wa wasu dakarun NAF 2 hukuncin dauri da aiki mai tsanani a gidan yari

Ambaliyar kogin ta jawo tsaiko wajen zirga-zirgar mutanen dake amfani da gadar Amba. Sai bayan janyerwa ruwan ne jama'a suka samu damar amfani da gadar.

Wani mazaunin unguwar Tudun Makama, Umar Mai Unguwa, ya ce bai taba ganin ambaliyar irin wannan ba a shekaru 20 da suka gabata.

Shugaban karamar hukumar Lafia, Muazu Maifata, ya kai ziyarar gani da ido domin ganin barnar da ambaliyar ruwa ta yi tare da daukan alkawarin bayar da tallafi ga wanda abin ya shafa.

Kazalika, gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ziyarci sassan da ambaliyar ta fi shafa tare da yin gargadi a kan jibge shara da yin gini a kan magudanan ruwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel